Bayan wuya sai dadi: Al'ummar Najeriya za su sharbi romo a shugabancin Buhari karo na biyu - Akande

Bayan wuya sai dadi: Al'ummar Najeriya za su sharbi romo a shugabancin Buhari karo na biyu - Akande

Wani dan majalisar dokoki ta jihar Legas, Mista Victor Akande, a yau Alhamis ya bayyana cewa, mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu kan karagar mulkin kasar nan zai tabbatar da jin dadi da sharbar romo ta talakawansa.

A yayin da mai hakuri shi yake dafa dutse har ma ya sha romon sa kuma ya gyatse, Mista Akande ya bayyana cewa, jagorancin shugaba Buhari karo na biyu za ya kasance lokaci na jin dadi da al'ummar kasar nan za ta ribaci hakurin da ta yi a baya.

Mista Akande wanda ke wakilcin shiyyar Ojo a majalisar dokoki ta jihar Legas, ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyin 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa a yau Alhamis cikin babban birnin na Legas.

Buhari yayin mallakar takardun bayyana kudirin takara
Buhari yayin mallakar takardun bayyana kudirin takara
Asali: Depositphotos

A cewarsa, dawo da kasar nan bisa turba da tafarki madaidaici ba za ya yiwu ba cikin shekaru uku kacal sakamakon yadda kasar ta rushe karkashin jagorancin gwamnatin PDP na tsawon shekaru 16 da suka shude.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin jam'iyyar APC a halin yanzu ta daura damara gami da dukufa wajen fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira da al'ummarta za ta sharbi romo sakamakon sadaukar da kai gami da hakuri mai tattare da juriya da ta yi.

KARANTA KUMA: Hukumar NECA ta bayyana yadda za a kawo karshen rashin aiki a Najeriya

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mista Akande ya yi bugun gaba tare da da kyautata zaton nasarar shugaba Buhari yayin babban zaben kasa na badi, inda ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba zai haifar da wani cikas ba.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dan takarar kujerar gwamna na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa za ya rungumi kaddara muddin ya sha kasa yayin babban zabe na 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel