Manyan jiragen ruwa 36 makare da kayan masarufi da man fetir na gab da shigowa Najeriya

Manyan jiragen ruwa 36 makare da kayan masarufi da man fetir na gab da shigowa Najeriya

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA, ta bayyana cewa akalla manyan jiragen ruwa da aka fi sani da suna jirgin dankaro guda talatin da shida (36) ne suka nufo Najeriya makare da tataccen man fetir da kayayyakin masarufi.

Majiyar Legit.com ta ruwaito hukumar NPA ta bayyana cewa ana sa ran jiragen zasu fara isowa ne daga ranar 6 ga watan Disamba zuwa ranar 29 ga watan Disamba, inda zasu sauka a tashoshin jiragen Tin Can Island da Apapa.

KU KARANTA: Malaman da El-Rufai ya fatattaka sun tabbatar da goyon bayansu ga Shehu Sani

Hukumar ta wallafa haka ne cikin rahotonta jaridanta na sati sati a ranar Alhamis, inda rahoton tace daga cikin jirage talatin shida akwai jirage shida dake dauke da tataccen man fetir, yayin da sauran jirage talatin ke dakon man jirgin sama.

Sauran kayayyakin dake kan jirage guda talatin sun hada fulawa, man disil, karafa, siga, da sundukai da dama. Bugu da kari hukumar NPA tace a yanzu haka akwai jirage guda goma sha shida dake jiran sauke kayan da suka dauko, jiragen na dauke da taki, da man fetir.

A wani labarin kuma, a ranar 23 ga watan Yuni ne wasu jiragen ruwa 34 cike da kayan man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani suka isa tashoshin jirgin ruwa na Apapa da Tin Can Island daga ranar Juma’a, 30 ga watan Yuni.

Hukumar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya (NPA) ce ta bayyana haka inda tace akalla shida daga cikin jiragen 34 na dauke da man fetur, yayin da sauran 25 ke dauke da alkama, mai, sundukan kayyayaki, daskararen kifi, waken suya, taki, da kuma karafuna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel