Tsohuwar zuma: Oyegun ya tsoma baki a rikicin APC
Cif John Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya jaddada bukatar hadin kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC domin samun nasara a zaben 2019, a yayin da yake korafi a kan masu kawowa jam'iyyar tangarda.
Ya yi gargadin cewar akwai babban aiki a gaban APC cikin watanni biyu da rabi kafin zabukan shekarar 2019 tare da yin roko ga mambobin jam'iyyar a kowanne mataki a kan bukatar samun hadin kai da zaman lafiya domin cigaban jam'iyya.
Oyegun, tsohon gwamnan jihar Edo, na wadannan kalamai ne a yau, Laraba, yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja.
Oyegun ya nuna damuwarsa da rikicin a kan rikicin da jam'iyyar APC ke fama da shi tun bayan kammala zabukan fidda 'yan takara a fadin jihohin kasar nan.
DUBA WANNAN: Badakallar NEMA: Babu wanda ke shirin tsige Osinbajo - Majalisa
"Maganar gaskiya bana jin dadin halin da jam'iyyar APC ke ciki. Babu wani dan APC na kirki da zai ce yana jin dadin abubuwan dake faruwa a jam'iyyar," a kalaman Oyegun.
Kazalika ya yi kira ga kowanne bangare da ya zama mai sadaukar wa don jam'iyyar APC ta samu zaman lafiya.
"Rokona daya ne ga duk mambobin jam'iyya ta; su yi hakuri domin a samu zaman lafiya da zai bamu damar tunkarar zabukan shekarar 2019 cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
"Ba abin boyewa bane cewar akwai matsaloli a cikin tafiyar jam'iyyar APC. Amma duk da haka naji dadin kafa kwamitin sulhunta fusatattun 'yan APC da uwar jam'iyya ta yi. Na hadu da mambobin kwamitin yayin wata tafiyar kasuwanci da ta kai ni yankin kudu maso gabas, kuma ina da karfin gwuiwar cewar zasu yi nasara a aikin da uwar ta basu.
"Amma duk da haka ya zama wajibi na yi kira ga mambobin mu a kan muhimmanci da bukatar samun zaman lafiya. Abinda ya kanata mu mayar da hankali a kai shine batun tunkarar zabe a watan Fabrairu na shekarar 2019," a cewar Oyegun.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng