Buhari ya gana da Shugaban kasar Switzerland kan dabarun ceto 'Yan Matan Chibok

Buhari ya gana da Shugaban kasar Switzerland kan dabarun ceto 'Yan Matan Chibok

A jiya Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da takwaransa na kasar na Switzerland, Alain Berset, a birnin Katowice na kasar Poland inda suka tattauna kan batutuwa da dabaru na ceto ragowar 'yan Matan Chibok.

Wannan ganawar tsakanin shugabannin kasashen biyu ta gudana ne a wani bigire na daban da taron Majalisar dinkin Duniya kan sauyi yanayi da yake ci gaba da gudana a kasar Poland kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugabannin biyu sun gana kan hanyoyi da dabaru na tabbatar da ceto ragowar 'yan Matan Chibok a bisa bibiyar tafarki dangane da yadda aka samu nasarar ceto wasu daga cikin 'Yan Matan a lokutan baya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan lamari na samun nasarar ceto bai takaita kadai kan 'yan Matan ba, domin kuwa ya hadar da dukkanin wadanda kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta yi garkuwa da su a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Buhari ya gana da Shugaban kasar Switzerland kan dabarun ceto 'Yan Matan Chibok

Buhari ya gana da Shugaban kasar Switzerland kan dabarun ceto 'Yan Matan Chibok
Source: UGC

A yayin tunatar da mai karatu, kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta yi garkuwa da kimanin Dalibai 276 na makarantar Mata da ke garin Chibok a jihar Borno tun a watan Afrilun shekarar 2014 karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

Buhari cikin wata sanarwa da sanadin hadiminsa kan hulda da manema labarai, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa, gwamnatin sa ba za ta gaza ba wajen ceto ragowar 'yan Matan Chibok da ke kangi na garkuwa a hannun kungiyar ta'adda ta Boko Haram.

KARANTA KUMA: 2019: Obasanjo, Atiku, Secondus sun sake ganawa a garin Abuja

Kazalika shugaban kasar ya yabawa ya gwamnatin kasar Switzerland dangane da muhimmiyar rawa da ta taka wajen ceto wasu daga cikin 'yan Matan a lokutan baya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaba Buhari ya kuma aiwatar da ganawa ta daban tsakanin sa da shugaban kasar Poland, Andrzej Duda da Firai Ministan kasar, Mateusz i Morawiecki dangane da kalubalai na sauyin yanayi da ke fuskantar nahiyyar Afirka ta Yamma musamman a yankunan gabar tafkin Chadi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel