Naira tiriliyan 20 sun yi ɓatan dabo a tsakanin CBN, NIPOST da ofishin sakataren gwamnati

Naira tiriliyan 20 sun yi ɓatan dabo a tsakanin CBN, NIPOST da ofishin sakataren gwamnati

Har zuwa yanzu an gagara samun gamsashshen bayanai game da inda makudan kudade da suka kai naira triliyan ashirin (N20,000,000,000,000) suka shiga a tsakanin wasu hukumomin gwamnatin tarayya duk da cewa an bi dukkanin matakan da suka dace wajen samun bayanan.

A ranar 31 ga watan Yuli ne wata kungiya mai zaman kanta, ICIR ta mika takardar jin bahasin inda makudan kudaden suka shiga ko kuma jin yadda aka kashesu ga ofishin sakataren gwamnati, babban bankin Najeriya, hukumar aika sakonni NIPOST da kuma kamfanin dake cinikayya tsakanin bankuna.

KU KARANTA: Yansanda sun yi ram da maigadin makabarta ya kwakulo gawar mutum daga cikin kabari

Kungiyar ta nemi samu masaniya game da wasu kudade da bankunan Najeriya suka biya, da kuma jama’an dake hulda da hukumar NIPOST suke biya, wanda aka fi sani da suna Stamp Duty a turance.

A cewar majiyar Legit.com a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2016, kudaden nan sun kai naira 20,000,000,000,000, amma bayan kimanin watanni biyu, har yanzu babu gamsashshen bayani da hukumomin gwamnati suka mayar ma kungiyar.

Sai dai NIPOST da NIBSS sun ki bada amsan bukatar da kungiyar ICIR ta aike mata, amma ofishin sakataren gwamnatin Najeriya cikin wata wasika data aika ma kungiyar tace kamata yayi ta aika ma hukumar tattara kudaden haraji ta kasa, FIRS, wannan bukata.

“Sakamakon cikakken nazarin wasikar da kuka aiko mana ta hannun mashawarcinku akan harkar sharia J.O Obule, ofishin sakataren gwamnati na ganin hukumar tattara kudaden haraji na kasa, FIRS ce tafi dacewa ta amsa tambayoyinku.

“Saboda haka muna sanar daku mun mika bukatunku zuwa hukumar FIRS, don haka muna shawartarku daku bi diddigin wasikar a hannun FIRS kai tsaye.” Inji wasikar data fito daga ofishin sakataren gwamnati.

Sai dai ita ma FIRS ta daura mayar da kungiyar ga hukumar NIPOST, domin kuwa a cewarta bata karbar kudin stamp duty daga hannun NIPOST, sai dai har zuwa lokacin tattara rahoton nan NIPOST bata bada amsa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

\Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel