Gwamnonin Kudu maso Gabas sun halarcin taron mu na Sokoto - Inji Jam’iyyar PDP

Gwamnonin Kudu maso Gabas sun halarcin taron mu na Sokoto - Inji Jam’iyyar PDP

- Jam’iyyar PDP ta karyata rade-radin cewa Gwamnonin Kudu ba su halarci gangamin da tayi ba

- Darektan yada labarai na Jam’iyyar ya musanya wannan jita-jita inda yace sam ba gaskiya bane

- Jam’iyyar ta shirya wani babban taro shekaran jiya inda kuma ake sa rai za a cigaba da zagaye

Gwamnonin Kudu maso Gabas sun halarcin taron mu na Sokoto - Inji Jam’iyyar PDP

Maganar cewa ana rikici da Gwamnonin PDP ba gaksiya bane inji Ologbondiyan
Source: Twitter

Mun ji cewa babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya watau PDP tayi watsi da rade-radin da ake yi na cewa Gwamnonin ta da ke Kudu maso Gabashin Kasar nan ba su halarci taron farko na yakin neman zabe da aka fara a makon nan ba.

Kwamitin yakin neman zaben PDP a 2019 ta fitar da jawabi inda ta musanya jita-jitan da ke yawo na rashin jituwa tsakanin Atiku Abubakar wanda ke rikewa Jam’iyyar tuta a babban zaben 2019 da kuma wasu manyan Gwamnonin ta.

Kola Ologbondiyan wanda shi ne Darektan yada labarai na Jam’iyyar ya bayyana wannan a jiya Talata 4 ga Watan Disamba a Abuja. Ologbondiyan yace wasu Gwamnonin Kudancin Kasar nan sun halarci taron da aka yi Ranar Litinin a Sokoto.

KU KARANTA: Za a yi zaben gaskiya da adalci a 2019 inji Ministan harkokin waje

Daga cikin Gwamnonin da su ka halarci wannan taro daga Kasar Inyamurai akwai Gwamna Dave Umahi (Ebonyi), sai Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) da kuma Gwamna Okezie Ikpeazu (Abia). Ologbondiyan yace kan ‘Yan PDP duk a hade yake.

A jawabin na Mista Ologbondiyan, ya bayyana cewa PDP ta shirya yawon yakin neman zaben ne a kowane sashe na Kasar. Nan gaba kadan dai jirgin yakin neman zaben na PDP zai shiga har cikin Kudancin Najeriya inji Darektan na PDP.

Babban Jami’in na PDP yace kusoshin Jam’iyyar da ke Yankin Sokoto, Zamfara, Kebbi, Jigawa, Katsina, Kano da Kaduna ne su ka halarci taron Sokoto. A Ranar Laraba kuma PDP za ta sake wani taron a Jihar Kwara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel