Zaben 2015: Ni da Adamu Mu’azu mu ka lallashi Goodluck Jonathan – Bala Na’Allah

Zaben 2015: Ni da Adamu Mu’azu mu ka lallashi Goodluck Jonathan – Bala Na’Allah

- Sanata Bala Na’Allah ya bayyana cewa su su ka lallashi Jonathan ya amince da zaben 2015

- Na’Allah yace shi da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Adamu Muazu su ka yi wannan aiki

- Wannan akasin abin da tsohon Shugaban Kasar ya fada ne a littafin da ya rubuta kwanaki

Zaben 2015: Ni da Adamu Mu’azu mu ka lallashi Goodluck Jonathan – Bala Na’Allah
Ibn Na’Allah yace shi da Muazu su ka rarrashi Jonathan game da zaben 2015
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Bala Ibn Na’Allah yayi ikirarin su ne su ka lallabi tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya hakura da zaben 2015 inda ya sha kashi a hannun Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC.

Sanatan yace shi da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa watau Ahmad Adamu Muazu ne su ka shawo kan tsohon Shugaban kasar har yayi na’am da zaben da aka gudanar a 2015 a Kasar, akasin abin da Dr. Jonathan ya bayyana.

KU KARANTA: Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019

Babban ‘Dan Majalisar wanda yake wakiltar Yankin Jihar Kebbi a karkashin Jam’iyyar APC ya bayyana abin da ya sha ban-ban da abin da Jonathan ya rubuta a littafin sa da aka kaddamar a Watan jiya mai suna ‘My Transition Hours’

Na’Allah yace yana Garin Kebbi ne Shugaban PDP na kasa, Mu’azu ya kira sa a waya ya nemi su tafi Birnin Tarayya Abuja domin su ga Jonathan, su kuma nuna masa cewa ya amince da sakamakon zaben wanda ya nuna za su sha kashi.

A baya kun ji cewa ‘Dan takarar Shugaban Kasa a PDP, Atiku Abubakar ya tofa albarkacin bakin sa da maganar da ake yi na cewa an kirkiro wani mai kama da Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Sudan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel