Jami'ar jihar Kano za ta fara koyar da ilimin likitanci da karin wasu 2

Jami'ar jihar Kano za ta fara koyar da ilimin likitanci da karin wasu 2

Jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Kano da ke garin Wudil (KUST) ta sanar da fadada harkokin bayar da ilimi zuwa na likitanci, lafiyar dabbobi, da kimiyyar hada magunguna.

Shugaban jami'ar, Farfesa Shehu Alhaji Musa, ya sanar da hakan yayin kafa kwamitin da zai tsara yadda za a fara karatu a sabbin tsangayoyin.

A wata sanarwa da mai dauke da sa hannun Alhaji Sa'idu Abdullahi Nayaya, mataimakin magatakarda mai kula da hulda da jama'a na jami'ar, jami'ar ta sanar da manema labarai shirinta na bude tsangayoyin bayar da ilimin likitanci, kimiyyar hada magunguna, da kuma na ilimin kula da lafiyar dabbobi.

Jami'ar jihar Kano za ta fara koyar da ilimin likitanci da karin wasu 2
Jami'ar jihar Kano za ta fara koyar da ilimin likitanci da karin wasu 2
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Babban magana: Kotu ta daure wasu mutane biyu saboda satar wayar alkali

Farfesa Musa ya bayyana cewar tuni shirye-shirye su ka yi nisa wajen ganin an samu a cikin garin Wudil da jami'ar za ta yi amfani da shi a matsayin asibitin koyarwa.

Ya kara da cewa tuni shugaban gudanarwa na jami'ar, Alhaji Aliko Dangote, ya yi alkawarin bayar da gudunmawa wajen gina asibitin koyarwa a garin Wudil.

Kazalika ya yabawa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa irin gudunmawar da yake bawa jami'ar ta kowanne fanni.

Daya daga cikin mambobin kwamitin da jami'ar ta kafa, Kabir Muhammad; tsohon kwamishinan lafiya a jihar Kano, ya yabawa jami'ar bisa wannan kokari, tare da bayar da tabbacin cewar zasu yi aiki tukuru domin sauke nauyin da aka dora ma su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel