Kudin makamai: Dole fa sai kayi bayani - Kotu ta shaidawa Shekarau

Kudin makamai: Dole fa sai kayi bayani - Kotu ta shaidawa Shekarau

- Lauyan tsohon gwamna jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya nemi kotu tayi watsi da tuhumarsa da akeyi na almundahanar N950m

- Lauyan Shekarau ya nemi hakan ne saboda rashin hallartar zaman kotu da lauyan EFCC bai yi ba a yau

- Sai dai kotun tayi watsi da bukatan na Shekarau inda ta ce EFCC ta rubuta wasika inda ta bayyana dalilin rashin hallartan kotun kuma ta nemi da daga shari'ar zuwa Janairun 2019

Babban kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta ki amincewa da bukatar lauyoyin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau da Ambassada Aminu Bashir Wali na watsi da karar da aka shigar na tuhumarsu da satar kudin al'umma.

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC ta gurfanar da Shekarau, Wali da Mansur Ahmed a kotun ne a ranar 24 ga watan Mayu bisa zarginsu da satar zunzurutun kudi Naira miliyan 950.

DUBA WANNAN: Yadda Saraki ya ci amanar mu a kan biyan bukatar sa - Tinubu

Sai dai a jiya da aka karanta shari'ar, lauyan hukumar EFCC, Johnson Ojogbane bai hallarci kotun ba.

Lauya mai kare Shekarau, J.S Okutepa ya sanar da kotu cewa ya rubutawa kotu wasika a ranar 30 ga watan Nuwamba inda ya ke nema a dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 27 ko 28 na watan Janairun 2019.

A yayin yanke hukuncinsa, mai shari'a A.L. Allagoa ya ce a cikin wasikar ta EFCC, lauyan hukumar ya ce zai tafi Kaduna inda zai hallarci wata shari'ar a kotun daukaka kara kuma tunda shar'arsa a ranar 3 ko 4 ga watan Disamba ne, yana da sauran rana guda domin ya bayyana a kotun.

"Na ga wasikar da EFCC inda ta ayyan cewa lauyanta zai hallarci wani shari'a kotun daukaka kara da ke Kaduna. Tunda shari'arsa a ranar 3 ko 4 ga watan Disamban 2018 ne, mu bari mu gani ko lauyan zai bayyana a gaban kotun," inji Allagoa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel