Babu sauran macizzai masu hadiye kudi a hukumar JAMB – Shehu Sani

Babu sauran macizzai masu hadiye kudi a hukumar JAMB – Shehu Sani

Dan majalisa mai wakiltar al’ummar Kaduna ta sanatoriyan tsakiya, Sanata Shehu Sani ya mayar da martani game da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na rage farashin jarabawar kammala sakadandari ta JAMB, da NECO.

Sanatan ya bayyana matakin a matsayin abinda ya kamata, inda yace hakan zai taimaka ma dalibai talakawa tare da rage musu radadin karatu, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter, inda yace gwamnatin Buhari ta tantanci yabo.

KU KARANTA: Wani Limamin Masallaci ya yi garkuwa da bawan Allah, har sai da ya kasheshi

Babu sauran macizzai masu hadiye kudi a hukumar JAMB – Shehu Sani
Jarabawar JAMB
Asali: Depositphotos

“Matakin rage farashin JAMB da na NECO da gwamnatin tarayya da dauka yayi daidai, hakan zai rage ma miliyoyin talakawa radadin karatu, haka zalika yadda kudaden shiga na hukumar JAMB suka karu abin a yaba ne. shugaban JAMB ya cancanci yabo, a yanzu na san babu sauran macizzai da kububuwa a JAMB.” Inji shi.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne Sanatan ya bankado wata badakala a hukumar JAMB, inda aka nemi wasu kudade daruruwna miliyoyi aka rasa, kuma da aka tambayi jami’ar da ake zargi da satar kudin sai tace ai macizzai ne suka hadiye kudin.

A wani labarin kuma, shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oleyede ya sanar da rage farashin jarabawar JAMB,NECO da BECE bayan tattaunawa da ministan ilimi Adamu Adamu, wanda ya bayyana cewa JAMB.

A cewar Farfesa Ishaq, tun bayan nadashi mukamin shugaban JAMB, ya tara ma gwamnati makudan kudade ta hannun hukumar ba kamar yadda aka saba yi a baya ba, inda ake kwashe kudaden da take tarawa, don haka ne ministan Ilimi yace ai ba’a kafa JAMB domin ta tara kudi ba, wannan yasa gwamnati ta rage farashin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel