Matan da su ke wakiltar Mazabar su a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa yanzu

Matan da su ke wakiltar Mazabar su a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa yanzu

Yanzu haka ana fama da karancin Mata a Majalisun Najeriya. A Majalisar Dattawa dai ana da Mata 6 ne kurum cikin Sanatoci fiye da 100 da ake da su a Kasar. Mun kawo jerin wadannan Mata da ke Majalisar Dattawan Kasar.

Matan da su ka wakilci Mazabar su a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa yanzu

Sanata Biodun Olujunmi mai wakiltar Kudancin Jihar Ekiti
Source: UGC

Daga cikin Matan da ake da su a Majalisar Dattawa, 1 ce kacal ta fito daga Arewa. Haka kuma Jam’iyyar APC ta samu Sanatoci 3 ne yayin da ita ma PDP ta samu Sanatoci mata 5 kafin a tsige Sanata 1 daga Majalisar kwanaki.

Ga dai Sanatocin nan kamar haka:

1. Stella Oduah

Sanata Stella Oduah tana wakiltar Anambra ta Arewa a karkashin Jam’iyyar PDP mai hamayya a Kasar. Oduah ta taba rike Ministar sufurin jirgin sama a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

2. Rose Okoji Oko

Sanata Rose Oko tana wakiltar Yankin Arewacin Kuros-Riba ne a karkashin Jam’iyyar PDP mai adawa. Rose Oko ta wakilci Mazabar ta a Majalisar Wakilai ta Tarayya tsakanin 2011-2015.

3. Fatimat Raji-Rasaki

Sanata Fatimat Raji-Rasaki it ace ‘Yar Majalisar da ke wakiltar tsakiyar Ekiti a Majalisar Dattawan Najeriya. Sanata Rasaki ta samu kujerar ne a Jam’iyyar PDP kafin ta sauya-sheka a shekarar nan.

KU KARANTA: Buhari ba zai iya gyara Kasar nan cikin shekaru 4 ba – Sanata Tinubu

4. Biodun Olujunmi

Sanata Biodun Olunjumi tana cikin manyan Sanatocin Kasar, inda yanzu haka it ace Shugaban marasa rinjaye. Olujunmi ta dade tana wakiltar Kudancin Jihar Ekiti a Majalisar Dattawan.

5. Remi Tinubu

Sanata Olurenmi Tinubu tana cikin Matan da su ka dade a Majalisar Dattawa. Yanzu haka Sanatar ta Legas za ta nemi komawa Majalisa a karo na uku a karkashin Jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

6. Binta Garba

Sanata Binta Masi Garba ce ‘Yar Majalisar da ke wakiltar Adamawa ta Arewa a Majalisar Dattawa. Masi Garba ta wakilci Kaduna ta Kudu da kuma Yankin Machika a Majalisar Wakilai a baya.

7. Monsurat Jumoke Sunmonu

Sanata Monsurat Jumoke Sunmonu ta Jihar Oyo ta tsakiya ta samu kujerar ta APC ne kafin ta sauya sheka zuwa Jam’iyyar ADC. Kafin nan ta rike Kakakin Majalisar dokokin Jihar Oyo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel