Mata ta maye kujerar mijinta a majalisar dokikin jihar Cross River

Mata ta maye kujerar mijinta a majalisar dokikin jihar Cross River

Hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Cross River ta bawa Mrs Stella Nkoro na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP shaidan nasarar lashe zaben maye gurbi da aka gudanar a ranar 17 Nuwamba a mazabar Ikom II a jihar.

Jami'in zabe na jihar, Dr Frankland Briyai ya ce Nkoro ce 'yar takarar tilo da ta tsaya a zaben sabod haka ita ta lashe zaben.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa bayan rasuwar Simon Nkoro mijin Mrs Nkoro a watan Augustan wannan shekarar ne aka samu gurbi kuma yanzu matarsa ta cike gurbin.

Mata ta maye kujerar mijinta a majalisar dokikin jihar Cross Rivers

Mata ta maye kujerar mijinta a majalisar dokikin jihar Cross Rivers
Source: Twitter

Har ila yau, NAN ta ruwaito cewa Mrs Nkoro itace 'yar majalisa na biyu a shekarar 2018 da ta maye gurbin mijinta a majalisar jihar ta Cross Rivers bayan rasuwarsa.

DUBA WANNAN: Ma'aikatan kananan hukumomin Zamfara ne ma fi koma baya a albashi

"Ba a gudanar da zaben maye gurbin ba saboda babu abokan hammaya.

"Kamar yadda sashi na 41 na dokar zabe na shekarar 2010 ta nuna, Mrs Stella Nkoro itace wadda ta lashe zaben," inji shi.

Ya yi kira da wadda ta lashe zaben ta nuna halin dattaku wajen gudanar da ayyukan ta a matsayin 'yar majalisar jihar.

"Yan da aka fara yakin neman zabe, ina kira ga ku 'yan siyasa ku gudanar da harkokinsu bisa ka'ida saboda a gudanar da sahihiyar zabe cikin lafiya da kwanciyar hankali a Cross River a shekarar 2019," inji shi.

A yayin da take jawabi, Nkoro ta mika godiyarta ga INEC da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen ganin an samu nasarar zaben ta, ta kara da cewa za ta dora daga inda mijinta ya tsaya wajen yiwa al'ummar yankinta hidima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel