Boko Haram: Mayaƙa sun ƙone wata babbar Gonar Shinkafa a jihar Borno

Boko Haram: Mayaƙa sun ƙone wata babbar Gonar Shinkafa a jihar Borno

Mun samu cewa Manoma a karamar hukumar Jere ta jihar Borno, sun yi koke dangane da yadda 'yan ta'adda da ake zargin mayakan boko haram ne suka kone wata babbar gonar Shinkafa kurmus.

Shugaban kungiyar Manoma da 'yan kasuwar Shinkafa na jihar ta Zabarmari, Alhaji Hassan Muhammad, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai na jaridar Daily Trust a jiya Litinin.

A yayin zayyana girman wannan asara da Manoman suka fuskanta a halin yanzu, Bulaman Zabarmari, Bulama Auwal Hassan, ya bayyana wannan lamari a matsayin mafi kololuwar girma ta fuskar zalunci.

Boko Haram: Mayaƙa sun ƙone wata babbar Gonar Shinkafa a jihar Borno
Boko Haram: Mayaƙa sun ƙone wata babbar Gonar Shinkafa a jihar Borno
Asali: Getty Images

Bulama kamar yadda shafin jaridar ta Daily Trust ta ruwaito ya kuma zayyana cewa, akwai yiwuwar wannan lamari zai janyo barazana ta yunwa da kuma karancin matukar ba a tashin tsaye an farga ba.

KARANTA KUMA: Harin Buni Gari : Gawarwakin Soji 2 sun sake bayyana a jihar Yobe

Dangane da aukuwa wannan mummunan lamari, mafi akasarin Manoman yankin garrin Jere sun bayyana korafe-korafen su na salwantar abin dogaro da ayanzu ya dakusar da burace-buracensu na samun arziki mai yalwa na amfanin gona da ya dara na bara.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a makon da ya gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa,gwamnatin sa ta sha alwashin yiwa Manoma waiwaye na arziki donin rangwanta ma su dangane da annobar ambaliyar da ruwa da ta auku cikin wasu jihohin kasar nan a Daminar bana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel