Babu wanda Atiku ya fada ma cewa ya karbi bizan Amurka – Jami’in kungiyar kamfen

Babu wanda Atiku ya fada ma cewa ya karbi bizan Amurka – Jami’in kungiyar kamfen

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar, bai taba fada ma wani cewar an bashi bizan Amurka ko kuma yana shirin zuwa Amurka ba wani babban jigo a kungiyar kamfen dinsa ya bayyana a jiya.

Babban jami’in, wanda ya jagoranci daya daga cikin manyan kungiyoyin kamfen din Atiku, ya bayyana lamarin yamadidi da ake akan batun karban bizan Atiku da tafiyarsa a matsayin abun alawadai tunda dai tsohon mataimakin shugaban kasar bai yi zancen haka da kowa ba.

Babu wanda Atiku ya fada ma cewa ya karbi bizan Amurka – Jami’in kungiyar kamfen

Babu wanda Atiku ya fada ma cewa ya karbi bizan Amurka – Jami’in kungiyar kamfen
Source: Facebook

Jigon wanda ya kasance tsohon ministan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fada ma Vanguard kan sharidin sirrinta sunansa cewa Atiku ba mutun ne da zai yi bikin mallakar biza ba domin ya zagaye kasashen duniya da dama tsawon shekaru da dama.

KU KARANTA KUMA: An hana kowa yin dawafi sai masu nakasa a Ka'aba

Da yake martani ga ikirarin jam’iyyar adawa na cewa Atiku na tsoron zuwa Amurka don gudun kada a kama shi kan rashawa, yayi bayanin cewa babu wani shari’a akan tsohon mataimakin shugaban kasar, cewa idan har akwai wani abut oh kasar zata tayar da zancen.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Injiniya Buba Galadima yana cikin wadanda ke yi wa PDP aiki wajen ganin an tika Shugaba Muhammadu Buhari da kasa a zaben da za ayi a shekarar 2019.

Buba Galadima wanda ya taba rike Sakatare na tsohouwar Jam’iyyar nan ta CPC mai adawa a 2011 ya bayyana dalilin da ya sa yake tare da Atiku Abubakar na Jam’iyyar hamayya. Galadima yana cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku.

Injiniya Buba Galadima dai shi ne ya jagoranci Kungiyar ta-ware na r-APC kafin su narke su shigo cikin tafiyar Jam’iyyar PDP. Galadima ya fadawa BBC Hausa cewa abubuwa sun sukurkuce ainun a Najeriya a mulkin Shugaban kasa Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel