Da ɗumi ɗumi: An naɗa sabon Kaakakin majalisar dokokin jahar Katsina

Da ɗumi ɗumi: An naɗa sabon Kaakakin majalisar dokokin jahar Katsina

Majalisar dokokin jahar Katsina ta zabi sabon shugaban majalisa wanda aka fi sani da suna Kaakakin majalisa, Alhaji Tasi’u Maigari a ranar Litinin 3 ga watan Disamba, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Legit.com ta ruwaito Maigari ya zamo sabon Kaakaki ne bayan dagawar likafar da tsohon kaakakin majalisar Abubakar Kusada ya samu, inda ya lashe zaben cike gurbi na kujerar dan majalisa mai wakiltar Kusada/Kankia da Ingawa a majalisar wakilan Najeriya da aka yi a watan Nuwamba.

KU KARANTA: Wasu ingantattun hanyoyi guda goma da Buhari ya kirkiro don hana jami’an gwamnati satar kudi

Da ɗumi ɗumi: An naɗa sabon Kaakakin majalisar dokokin jahar Katsina

Majalisa
Source: UGC

Sabon Kaakakin bai samu adawa daga ko dan majalisa daya ba, inda duka yan majalisu guda Talatin da biyu, 32, suka amince da shi ba tare da nuna hamayya ba, majalisar na da yan majalisa guda Talatin da hudu, 34 ne.

Sabon Kaakaki Tasiu Maigari ya fito ne daga karamar hukumar Zango ta jahar Katsina dake shiyyar mazabar Daura, inda yake wakiltar al’ummar karamar hukumar Zango.

Dan majalisa mai wakiltar Matazu, Ibrahim Dikko ne ya fara tayar da maganan a zaman majalisar, inda ya nemi majalisar ta zabi sabon Kaakaki, nan da nan dan majalisa daga Baure Sani Lawan ya goyi bayan bukatar da Dikko, anan aka zabo Maigari.

Ba tare da bata lokaci ba akawun majalisar Musa Bakori ya rantsar da sabon Kakaki Tasiu Maigari wanda ya fito daga jam’iyyar APC, daga nan kuma majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 14 ga watan Janairu 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel