Jerin sunayen sabbin kwamishinoni guda 11 a jahar Nassarawa da majalisa ta tantance

Jerin sunayen sabbin kwamishinoni guda 11 a jahar Nassarawa da majalisa ta tantance

Majalisar dokokin jahar Nassarawa ta tabbatar da sahihancin wasu mutane guda goma sha daya da gwamnan jahar Umar Tanko Al-Makura ya tura mata sunayensu don tantancesu kafin ya tabbatar dasu a matsayin sabbin kwamishinoninsa.

Legit.com ta ruwaito Kaakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi ne ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Litinin, 3 ga watan Disamba, a babban birnin jahar Nassarawa, Lafiya.

KU KARANTA: Wasu ingantattun hanyoyi guda goma da Buhari ya kirkiro don hana jami’an gwamnati satar kudi

Sunayen kwamishinoni masu jiran gadon sun hada da; Hajiya Halima Jabiru, Salisu Abubakar Haske, Victor Terrah, Musa Suleiman, Hajiya Jamila Sarki , Uwargida Mary Enwongulu, Dakta Roseline Kela da Hajiya Sa’adatu Yahaya.

Sauran sun hada da Hudu Yamba Agidi, Dakta Clement Uhembe da Mohammed Bashir Aliyu, kamar yadda kaakakin majalisar ya karantosu a gaban sauran yan majalisu da suka halarci zaman.

Da yake jan kunne a garesu, Kaakakin ya gargadi sabbin kwamishinonin akan su kasande masu gaskiya, adalci, rikon amana ba tare da nuna son kai, ko kuma bambamcin addini dana kabilanci ba idan an nadasu mukaman,

Sa’annan Kaakakin yayi kira a garesu da suyi amfani da iliminsu wajen ganin sun bada gudunmuwa wajen cigaban jahar, daga karshe ya shawarcesu da su kasance masu tsantsani da rikon amana wajen kulawa da kudaden al’ummar jahar.

Daga karshen karshe kuma Kaakaki Balarabe ya bayyana manufar majalisar na cigaba da samar da sahihan dokoki da zasu taimaka ma al’ummar jahar Nassarawa tare da kyautata rayuwarsu.

Idan za’a tuna a ranar 27 ga watan Nuwamba ne Gwamna Al-Makura ya aika da sunayen mutane goma sha daya gaban majalisar dokokin jahar don tantancesu kafin ya nadasu mukaman kwamishinoni bayan ya fatattaki wasu kwamishinonin daga mukamansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel