An gargadi limaman Coci da ba za su daina luwadi ba su ajiye aiki

An gargadi limaman Coci da ba za su daina luwadi ba su ajiye aiki

- A makon da ya wuce, Fafaroma Francis ya nuna damuwarsa a kan wasu bangare na masu 'yan luwadi

- Shuguban mabiyar darikar kotolika na duniya ya yi wannan jawabin ne a hirar da akayi dashi a cikin wani litaffi da aka wallafa

- Darikar Katolika da amince da cewa sha'awar irin jinsi daya ba laifi bane amma ta ce saduwar mutane jinsi guda zunubi ne

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya ce cocin ba za ta amince da limamai masu sha'awan maza ko luwadi ba, inda ya kara da cewa zai fi zama alkhairi ga duk wani limami dan luwadi ya ajiye aikinsa a maimakon rayuwa cikin munafinci.

An gargadi limaman Coci da ba za su daina luwadi ba su ajiye aiki

An gargadi limaman Coci da ba za su daina luwadi ba su ajiye aiki
Source: Depositphotos

Duk da cewa a baya Fafaroman ya bukaci a tsaurara matakan tantance wadanda za a dauka a matsayin limaman coci, wannan jawabin da ya yi na cewa duk limaman da ba za su iya kame kansu ba su ajiye aikinsu shine wanda ya fi fitowa karara a kan batun.

DUBA WANNAN: Za mu sake dawowa: Fusatattun 'yan fashi sun aika takarda gidajen jama'ar da su ka gudu

Fafaroma Francis ya yi wannan jawabin ne a hirar da akayi da shi cikin wani litaffi mai suna 'The Strength of Vocation' wadda a cikin aka tattauna a kan kallubalen da ke tattare da rayuwar limaman cocin Katolika na rashin aure da saduwa.

A cikin litaffin, Fafaroma Francis ya ce batun luwadi a cocin abu ne da ya dade yana ci musu tuwa a kwarya. Ana sa ran za a kaddamar da littafin a cikin wannan makon a cikin harsuna daban-daban. Amma Reuters ta samu kofi guda na litaffin a cikin harshen Italiya.

'Batun sha'awar jinsi iri daya babban magana ne,' inji shi, inda ya kara da cewa ya kamata duk wanda za a horas a matsayin limaman coci su kasance mutane ne masu dattaku da kiyaye sha'awarsu kafin a amince da su.

Wannan batun ya shafi mata da ke son sadaukar da rayuwarsa wajen bautar Ubangiji.

Cocin Katolika da amince da cewa sha'awar irin jinsi daya ba laifi bane amma ta ce saduwar mutane jinsi guda zunubi ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel