Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland

Shugaba Muhammadu Buhari ya zanna da yan Najeriya mazauna kasar Poland a ranan Lahadi, 2 ga watan Disamba, 2018.

Mun kawo muku rahoton cewa Buhari zai bar Abuja domin zuwa birnin Katowice, kasar Poland, rana Asabar domin halartan taron gangamin duniya kan canjin yanayi karo na 24 na majalisar dinkin duniya wato UNFCCC.

Wannan taro na shugabannin duniya zai gudana ne daga rana 2 ga watan Disamba zuwa 5.

Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland

Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland
Source: Facebook

Game da cewar wadanda suka shirya taro, ana kyautata zaton kammala magana kan aiwatar da shawarwarin da ke cikin yarjejeniyar canjin yanayi da akayi a kasar Faransa wato "Yarjejeniyar Paris".

A taron, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai gabatar da jawabi kan irin namijin kokarin da gwamnatin Najeriya keyi wajen dakile canjin yanayi ta hanar aiwatar da ayyukan da ta shirya.

Bayan hakan, Buhari zai gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland. Kana zai gana da shugaban kasar Poland, Andrzej Duda da firam ministan kasar Mateusz Morawiecki.

Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland

Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland
Source: Facebook

Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland

Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland
Source: Facebook

Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland

Hotuna: Buhari ya gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland
Source: Facebook

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel