2019: Tawagar yakin neman zaben Atiku ta dira Sokoto

2019: Tawagar yakin neman zaben Atiku ta dira Sokoto

Kamar yadda ta sanar a jadawalin tsare-tsarenta na yakin neman zaben shugaban kasa, ayarin kamfen din dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP ya dira a jihar Sokoto, arewa maso yammacin Najeriya, domin kaddamar da kamfe din zaben Atiku.

Jam'iyyar ta PDP za ta fara kaddamar da yakin neman zabe ne a jihar Sokoto, kamar yadda darektan yada labarai na kamfen din Atiku kuma kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya sanar.

A sanarwar da kwamitin kamfen din Atiku ya fitar a jiya, Asabar, ya ce kwamitin yakin neman zaben zai tattauna da ma su zabe da niyyar nusar da su kalubalen da Najeriya ke fuskanta da kuma yadda Atiku ke shirin magance su.

2019: Tawagar yakin neman zaben Atiku ta dira Sokoto

Tawagar yakin neman zaben Atiku a Sokoto
Source: Facebook

A cikin sanarwar da ta fitar, PDP ta ce babu yankin da ya fuskanci koma baya a karkashin gwamnatin APC kamar yankin arewa maso yamma da shugaba Buhari ya fito tare da bashi kuri'u ma fi yawa a zaben shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Tsakanin Atiku da gwamnonin PDP: Har yanzu da sauran rina a kaba

"A cikin shekaru uku, babu wani cigaba da za a nuna shi da sunan cewar Buhari ya kawowa yankin arewa maso yamma. Duk gudunmawar da yankin ya bayar ta tashi a banza domin shugaba Buhari bai kara waiwayen yankin ba tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015," a cewar jam'iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel