Babu aiki, babu albashi: Akidar Boko Haram ce - ANSA ta yiwa gwamnatin tarayya raddi
Wata gamayyar kungiyar daliban Najeriya, "Alliance Of Nigerian Students Against Neo Liberal Attacks (ANSA)," ta ce barazanar gwamnatin tarayya na kin biyan malaman jami'o'i albashi muddin ba su janye yajin aiki ba, rashin tausayi ne da sanin ya kamata.
Hakan na kunshe ne cikin wata takarda da kungiyar ta fitar a jiya, Asabar, inda take zargin gwamnatin tarayya da kashe ilimi a makarantun Najeriya.
Tun ranar 4 ga watan Nuwamba ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki domin tilasta gwamnati sakin isassun kudade domin gyara ilimin jami'o'i.
Sai dai a wata takarda da hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) ta fitar zuwa ga shugabannin jami'o'in kasar nan, ta sanar da su cewar gwamnatin tarayya za ta yi aiki da dokar nan ta 'babu aiki, babu albashi" ga malaman jami'o'in dake yajin aiki.
Sai dai kungiyar ANSA ta yi Alla-wadai da wannan yunkuri na gwamnatin tarayya tare da bayyana shi da cewar akidar Boko Haram ce.
Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar daina biyan malaman jami'o'in albashi ne bayan sun gaza cimma daidaito a zaman sulhun da su ka yi.
DUBA WANNAN: Dan takarar shugaban kasa ya koma APC, ya goyawa Buhari baya
Kungiyar ASUU ta yi kaurin suna wajen tafiya yajin aiki. Kusan babu wata gwamnati ko shugaban kasar Najeriya da malaman jami'a ba su yiwa aikin ba.
ASUU na shiga yajin aikin ne a kan uzurin cewar gwamnatocin Najeriya ba sa warewa bangaren ilimi, musamman a matakin jami'a, isassun kudade. Lamarin da ta ce na barazanar durkusar da harkokin koyo da koyarwa a Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng