Lafiya Jari: Yawaita Zama yana janyo lahani na cututtukan Zuciya - Masana sun yi gargadi

Lafiya Jari: Yawaita Zama yana janyo lahani na cututtukan Zuciya - Masana sun yi gargadi

Za ku ji cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne wani kwararren Likitan kwalkwalwa da ke garin Abuja, Dakta Joe Ugwu, ya bayyana cewa, yawaitar zama wuri guda ba yana janyo barazana ta cututtukan da suka shafi zuciya.

Dakta Ugwu ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a babban birnin kasar nan tarayya inda ya yi gargadin cewa, zama wani yanayi ne da ke dakile duk wata gudanarwa da kai komo da ya kamata jikin dan Adam ya samu kama daga budewar tashohin jini zuwa ga aikace-aikacen gabbai da dukkanin kwayoyin halittu na sassan jiki.

Ya ke cewa, yawaita zama ya na dakile mu'amala a tsakanin kwayoyin halittu da ke da alhakin gudanar jini, narkewar maiko da rashin kai komo na dukkanin sunadarai da jikin dan Adam ke bukata.

Lafiya Jari: Yawaita Zama yana janyo lahani na cututtukan Zuciya - Masana sun yi gargadi
Lafiya Jari: Yawaita Zama yana janyo lahani na cututtukan Zuciya - Masana sun yi gargadi
Asali: UGC

Likitan da ke wani Asibitin Kudi a garin Abuja ya kuma bayar da shawara a bisa tafarki na kwarewa wajen kira ga Mutane da su rika motsa jikin su domin bunkasar lafiyarsu da ingancinta a madadin su lafke wuri guda.

Ya ci gaba da cewa, wannan hanya ita kadai ce tafarkin tsira da ke da tasirin gaske wajen yiwa jikin Dan Adam garkuwa tare da dakile kamuwa da cututtuka daban-daban ma su barazana ga kiwon lafiya.

KARANTA KUMA: Zan bayar da tallafi ga Manoman da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a bana - Buhari

Cikin wani binciken mai nasaba da wannan da aka wallafa a shafin yanar gizo na www.betterhealth.vic.gov.au ya bayyana cewa, baya ga yawaitar zama, yawaitar kwanciya na da nasaba ga miyagun cututtuka da suka hadar da ciwon zuciya, ciwon Daji watau Kansa da kuma ciwon Suga.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani bincike da aka wallafa a mujallar Jean & Hailes ya bayyana cewa, mace-mace a tsakanin Mata na ci gaba da ta'azzara a kasar Australia a sakamakon cututtukan hawan jini, ciwon suga, nauyi jiki da kuma ta'ammali a Sigari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel