Hukumar 'yan sanda ta bayyana su waye 'yan bindigar da su ka bulla a Sokoto

Hukumar 'yan sanda ta bayyana su waye 'yan bindigar da su ka bulla a Sokoto

- A jiya ne rahotanni su ka bayyana cewar wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana tare da kwace iko da karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto

- Hukumar 'yan sanda ta ce mutanen da ake magana a kansu, makiyaya da ke shigowa neman abinci duk shekara daga kasar Mali

- Sai dai wasu rahotannin sun yi ikirarin cewar haka wasu 'yan ta'adda ke shigowa cikin Najeriya ta iyakar mu da Nijar tare da daukan kananan yara da matasa domin ba su horo

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya na kasa, Jimoh Moshood, ya fitar, hukumar 'yan sandan ta ce mutanen da aka bayyana bullar su a Sokoto, makiyaya ne daga kasar Mali.

Moshood ya bayyana cewar makiyayan na shigowa jihar Sokoto duk shekara domin nemawa dabbobin su abinci.

A jiya, Juma'a, ne rahotanni su ka bayyana cewar an samu bullar wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ta kwace iko da karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Hukumar 'yan sanda ta bayyana su waye 'yan bindigar da su ka bulla a Sokoto

Hukumar 'yan sanda ta bayyana su waye 'yan bindigar da su ka bulla a Sokoto
Source: Twitter

A cewar rahotannin, kungiyar na dauke da muggan makamai sannan na yin wa'azi, lamarin da ya saka mazauna yankin cikin fargaba da tashin hankali.

Sai dai hukumar 'yan sanda ta ce tana sane da shigowar makiyayan yankin tun ranar Talata da aka fara ganinsu. Kazalika hukumar ta ce makiyayan ba su kasance barazana ga jama'a ba tare da karyata rahotannin da ke nuna cewar mutanen na bi kauyuka domin tilasta jama'a biyan zakka.

DUBA WANNAN: Ramuwar gayya: Sojoji sun tashi wata maboyar 'yan Boko Haram

Rundunar 'yan sandan ta bukaci jama'ar jihar Sokoto da kewaye da su kwantar da hankalinsu, su kuma cigaba da gudanar da al'amuran rayuwar su ba tare da wata fargaba ba.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar tun ba yanzu ba wasu 'yan bindiga ke shigowa karamar hukumar Tangaza me makwabtaka da Nijar tare da diban yara da matasa domin ba su horo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel