Siyasar Kano ta dau dimi: Har yanzu dai jiga-jigai Kwankwaso da Shekarau ke tada qura

Siyasar Kano ta dau dimi: Har yanzu dai jiga-jigai Kwankwaso da Shekarau ke tada qura

- Gangamin da aka yiwa Shekarau a Kano ya sanya jam'iyar adawa a wani yanayi

- A satin daya gabata ne aka shirya masa wannan gangami

- Gangamin ya samu halartar manyan yan jam'iya

Siyasar Kano ta dau dimi: Har yanzu dai jiga-jigai Kwankwaso da Shekarau ke tada qura

Siyasar Kano ta dau dimi: Har yanzu dai jiga-jigai Kwankwaso da Shekarau ke tada qura
Source: Depositphotos

A ranar Lahadin data gabata ne aka shiryawa tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau gangamin maraba da komawa jam'iyar APC a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.

Taron ya samu halarta shugaban jam'iyar Adam Oshiomhole, Barr Inuwa Abdulkadir, gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar, Sanata Kabiru Gaya tare da wasu manyan manya na jam'iyar.

Idan bamu manta ba a shekara ta 2014 Shekarau yabar jam'iyar APC ya koma PDP a sanadiyyar komawar Rabi'u Kwankwaso jam'iyar.

DUBA WANNAN: Har yanzu Buhari bai iya daukar mataki kan Shitu ba

Shekarau baiyi kasa a gwiwa ba a shekara ta 2018 ya karayin kaura ya koma gidan shi na asali wato APC biyo bayan komawar kwankwaso PDP.

Da yake tofa albarkacin bakin sa Shakarau yace yanada dalilin daya sanyashi komawa APC sannan ya kara da cewa jam'iyar ita zata lashe duk wasu mukamai a zaben 2019.

A wani loko kuma, an jiyo Kwankwaso yana koka wa da Bidiyon GAnduje yana dumbuzar Dala, inda yace badakalar abin kunya ce da ba kawai Kano ta zubda wa damutumci ba, har ma da Hausawa da Musulmi baki daya.

Gwamna Ganduje yace dai sharri ne, hadimansa kuwa sunce hada ma bidiyon aka yi.

Muddin dai ta tabbata Ganduje ya kasa tsallake wannan tarko, to kuwa Kano zata koma hannun Malam Shekarau ne, maimakon Kwankwasiyya.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel