Ramuwar gayya: Sojoji sun tashi wata maboyar 'yan Boko Haram
Hukumar sojin Najeriya ta ce ta tashi wata maboyar 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram a yankin karamar hukumar Gamboru Ngala a jihar Borno.
A sanarwar da hukumar sojin Najeriya ta fitar a shafinta na Tuwita, ta ce rundunar soji ta kai hari kan sansani biyu na 'yan ta'addar a yankin.
Sanarwar ta kara da cewar dakarun soji sun mamayi mayakan a daidai lokacin da su ke shirya kai hari, lamarin da ya sa su guduwa su ba makamansu, kayan abinci, da ragowar kayan amfani.
"A cigaba da biyayya ga umarnin shugaban rundunar soji ta kasa, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, da dakarun soji na Ofireshon Lafiya Dole, ke yi a kan kakkabe ragowar mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno, bataliyar soji ta 3 da ta 22 sun fara wani aikin atisaye daga ranar 29 ga watan Nuwamba, 2018.
"Jaruman dakarun sun gudanar da wani samame a sansani biyu da ke gadar Ngala da garin Gamboru a gabashin jihar Borno.
DUBA WANNAN: Sakon Buhari ga shugabannin kasashen gefen tekun Chadi
"Mayakan kungiyar Boko Haram da ke shirya kai hari sun gudu bayan hango dakarun soji na tunkarar maboyar su.
"Sun gudu sun bar kayan abinci da makamai da su ka hada da bindigu, alburusai da bama-bamai, da mota da kuma babura," a cewar sanarwar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng