Safarar kwaya: Kotun kasar Malaysia ta yankewa dan Najeriya hukuncin kisa

Safarar kwaya: Kotun kasar Malaysia ta yankewa dan Najeriya hukuncin kisa

Wata kotun kasar Malaysia ta yankewa wani dan Najeriya mai suna Sidrey Dike hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifin safarar kwaya.

Rahotanni sun bayyana cewar an samu Dike, mai shekaru 46, da laifin safarar sinadarin methamphetamine mai nauyin 700gm zuwa kasar ta Malaysia a shekarar 2017.

Alkalin kotun, Datuk Azman Abdallah, ya yanke wa Dike hukuncin bayan gaza gabatar da wasu hujjoji domin wanke kansa daga zargin da ake yi masa.

Safarar kwaya: Kotun kasar Malaysia ta yankewa dan Najeriya hukuncin kisa

Safarar kwaya: Kotun kasar Malaysia ta yankewa dan Najeriya hukuncin kisa
Source: Twitter

"Bayan sauraron hujjar ma su kara da wanda ake kara, kotu ta gamsu cewar wanda ake ake zargin ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi kuma ta yanke ma sa hukuncin kisa ta hanyar rataya," a kalaman Alkali Abdallah.

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar An kama wasu 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane su 7 bisa zarginsu da sace mataimakin kwanturola a hukumar kwastam, Justina Tanko, tare da kisan wani dan kasuwa, Chukwubuikem Ezenkwu.

Wadanda ake zargin su ne; Godspower Keenom, Zigabari Voonu, Oludofin Yakubu, Jastis Afangide, Dale Keliaga, Maxwell Barindom, da Tordi Barinaa. Rundunar babban sifeton rundunar 'yan sanda ta martanin gaggawa ce bisa jagorancin Abba Kyari ta yi nasarar cafke mutanen a yankin Onne a jihar Ribas.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Borno ta bawa sojoji 5 kyautar manyan motoci, hotuna

Wannnan ba shine karo na farko da kotun kasar Malaysia ke zartar da hukuncin kisa a kan 'yan Najeriya da ta samu da laifin safarar kwaya ba.

Rahotanni sun bayyana cewar ma su laifin sun karbi miliyan N5m kudin fansa kafin su saki jami'ar hukumar kwastam, Tanko.

Masu garkuwa da mutanen sun kashe dan kasuwar tare da jefa gawar sa a cikin wani tafkin ruwa duk da sun karbi miliyan N2.5m kudin fansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel