Ina adawa da Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea - Tinubu

Ina adawa da Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea - Tinubu

Kanwa Uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa kasancewarsa mai goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester ya sanya ya ke matukar adawa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Tinubu ya zayyana alakarsa da ilimin kwallon kafa yayin da fitaccen dan kwallon kafa na Najeriya kuma tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Mikel Obi, ya ziyarce har gida cikin daularsa da ke birnin Ikoyi a jihar Legas.

Dan wasan na Super Eagles da a halin yanzu yake taka leda shiyyar wasanni ta Chinese Super League, ya ziyarci jigon na jam'iyyar APC domin neman goyon bayansa dangane da shirin fitattu da zakakuran 'yan wasan kwallon kafa da za a fara gudanarwa cikin shekara mai gabatowa wanda gidauniyarsa ta Mikel Obi Foundation za ta daukin nauyin assasasawa.

Ina adawa da Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea - Tinubu

Ina adawa da Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea - Tinubu
Source: Instagram

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ya taka fagen nasara a fannika da dama, ya bayyana mamakinsa dangane da yadda Tinubu ke da ilimi daidai gwargwado akan harkar kwallon kafa baya ga kasancewarsa gogaggen dan siyasa.

KARANTA KUMA: Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 5 a jihar Enugu

Duk da kasancewar Obi tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Tinubu, wanda ya kuma kasance tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana tsananin adawarsa ga kungiyar kasancewarsa mai goyon bayan kungiyar Manchester United da dukkanin ke kasar Ingila.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya Alhamis kungiyar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ta nada Sanata Dino Melaye a matsayin kakakinta kuma jagoran hulda da al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel