Mataimakin Atiku Abubakar ya tabbatar da babu hannun Buhari a cikin matsalolin najeriya
Tsohon gwamnan jahar Anambra, kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Pter Obi ya bayyana ma duniya cewa babu hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen kirkiro matsalolin da kasar Najeriya ke fama dasu a yanzu.
Don haka a cewarsa bai kamata a dinga ganin laifin shugaba Buhari akan duk matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu ba, kai a cewar Peter Obi, babu wani mutum daya da za’a bayyana shi a matsayin matsalar Najeriya, sai dai kawai ace gadar matsalolin da akayi.
KU KARANTA: Wa’iyazubillahi: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga jigon APC saboda laifin wulakanta Al-Qur’ani
Majiyar Legit.com ta ruwaito Obi ya bayyana haka ne a garin Abakaliki, babban birnin jahar Ebonyi, inda yace akwai matsala matuka yadda kasashen da suke sa’annin Najeriya a shekarun baya suka tsere mata a duka bangarorin cigaba.
A cewar tsohon gwamnan, wadannan matsaloli abin kunya ne ga Najeriya, kuma ya kamata a dubasu da idon basira, domin a cewarsa lokaci yayi daya kamata a shawo kan matsalar, domin kuwa hatta a fafutukar da wasu keyi na ganin an raba kasarnan na daga cikin matsalar shugabanci.
“Ya zama wajibi Najeriya ta rungumi tsarin majalisar dinkin duniya na cigaban muradun karni, saboda hatta tsarin farko na samar da muradun karnin ma Najeriya bata cimmasa ba, ballantana kuma a fara maganan cigabansu.” Inji shi.
Sai dai kungiyar kwadago ta Najeriya, TUC ta yi kira ga shuwagabannin Najeriya da jama’an kasar dasu dage su yi duba ga halin da bangarorin siyasa, tattalin arziki, da ma zamantakewar suke ciki domin lalubo hanyoyin magance matsalolin da ake fama dasu.
TUC ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da shugabanta Bobboi Bala Kaigama ya fitar ne a ranar Alhamis, inda yace ya kamata gwamnati ta daina kashe makudan kudade wajen kula da yan siyasa, wadanda an zabesu ne don su bauta ma jama’a.
Don haka yace kamata yayi yan siyasa su dinga samar da ababen walwalan jama’a a Najeriya, kamar yadda suke zuwa kasashen turai suke ganin yadda jama’a ke moran ababen, irinsu wuta, ruwa, asibitoci, makarantu, sufuri da dai sauransu.
“Abin takaici ne yadda shuwagabanninmu ke wucewa kasashen waje suna jin dadi, amma basa iya kawo ma yan Najeriya ire iren ababen more rayuwan da suka samu a kasashen, ta yaya kasarnan ba zata fada cin tabarbarewar tattalin arziki ba bayan yan siyasa na kashe kudinsu wajen sayan gidaje Dubai, Amurka, Ingila da sauran kasashe?” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng