Kannywood: Za ayi babban bikin aure tsakanin wasu fitattun jaruman Fim masoya

Kannywood: Za ayi babban bikin aure tsakanin wasu fitattun jaruman Fim masoya

Biki iya biki, shagali iya shagali a yayin da wasu shahararrun jaruman fina finan Kannywood guda biyu masoya juna suka dauki gabaran tabbatar da soyayyarsu tare da kaunar juna ta hanyar dinke tsakaninsu da zama tare na har illa masha Allah, watau aure.

Wadannan jarumai na Kannywood da zasu auri junansu sune Sadik Zazzabi, fitaccen mawakin da fina finan Kannywood, da Maryam Booth, shararriyar jaruman fina finan hausa da aka fi saninsu da suna Kannywood.

KU KARANTA: Korarrun ma’aikatan jahar Kaduna sun shiga hannu bayan an kamasu suna yi ma El-Rufai Al-kunut

Kannywood: Za ayi babban bikin aure tsakanin wasu fitattun jaruman Fim masoya

Sadik da Maryam
Source: UGC

Legit.com ta ruwaito jaruman biyu sun dade suna soyayya da junansu, amma soyayyar bata fito fili ba har sai a yan kwanakin nan da aka fara ganin hotunansu suna yawo a shafukan sadarwar zamani na yanar gizo, hotunansu na shirin biki kenan.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne wata kotu dake jahar Kano ta daure Sadik saboda ya fitar da wata waka, wanda ake ganin wakar siyasace da ya yi ta don goyon bayan tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sai dai wakar ta sosa ma gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje rai saboda hamayyar dake tsakaninsa da tsohon maigidan nasa Kwankwaso, wanda haka ne ya sabbaba hukuma tace fina finai ta jahar Kano ta gurfanar da shi a gaban kotu akan zarginsa da laifin sakin wakar a kasuwa ba tare da ya jira ta tace wakar ba.

Kannywood: Za ayi babban bikin aure tsakanin wasu fitattun jaruman Fim masoya

Amarya da Ango
Source: UGC

Ita kuwa jaruma Maryam Booth an haifetane a ranar 8 ga watan Oktoban 1993 a jahar Kano, iyayenta Ado Muhammed da Zainab Booth wanda itama fitacciyar jarumar fina finai ce, haka zalika yayanta Ahmed Booth ma jarumin fim ne.

Maryam ta shahara finai finai da dama, musamman a fim din Dijangala, Alawiyya, Ankwa, Bani Adam, Dare, Baya, Halisa, Garin Gaka, Mai Lita da sauransu. Muma daga nan muna tayata masoyan fatan alheri, tare da adduar Allah ya basu zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel