Sakon Buhari ga shugabannin kasashen gefen tekun Chadi

Sakon Buhari ga shugabannin kasashen gefen tekun Chadi

Shugaba Muhammadu Buhari ya kalubanci ragowar shugabannin kasashen gefen tekun Chadi (LBC) a kan kara rubanya kokarinsu a bangaren yaki da 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram.

Buhari ya yi wannan kira ne a yau, Alhamis, yayin halartar taron shugabannin kasashen gefen tekun Chadi a birnin N'Dajamena.

"Ba zamu saurara ko mu bar makiya yankin mu su sukurkuta zaman lafiya a kasashen mu ba. Dole mu kara kokarinmu domin korar ta'addanci daga yankinmu."

"Dole mu tashi tsaye wajen samar da zaman lafiya da cigaba mai dorewa. A wannan gaba ne nake bukatar mu hada karfi da karfe domin ganin mun kakkabe ragowar 'yan ta'adda daga yankin mu," a kalaman Buhari.

Sakon Buhari ga shugabannin kasashen gefen tekun Chadi

Shugabannin kasashen gefen tekun Chadi
Source: Twitter

Taron ya samu halartar shugabannin kasashen Chadi, Nijar, da Kamaru.

A baya legit.ng ta sanar da ku cewar a yau, Alhamis, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi zuwa N'Dajamena, babban birnin kasar Chadi, domin shugabantar taron shugabannin kasashen Afrika dake da makwabtaka da tekun Chadi (LBC).

DUBA WANNAN: Abu biyu kacal gwamnatin Buhari ta samar - PDP

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta rawaito cewar Buhari ya yi amfani da matsayinsa na shugaban kungiyar kasashen wajen kiran taron domin tattauna yadda za a samu zama zaman lafiya mai dorewa a rukunin kasashen LBC dake fama da hare-haren 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa da Femi Adesina, karamin kakakin shugaba Buhari, ya fitar a Abuja ya ce za a yi taron ne yau, Alhamis, a N'Dajamena.

Adesina ya bayyana cewar an gayyaci shugaban kasar Benin zuwa wurin taron saboda kasar sa ta bayar da gudunmawar sojoji domin yakar aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

A cewar Adesina, taron na kwana daya zai tattauna yanayin tsaro a tsakanin kasashen da niyyar samar da hanyoyin da za a bi domin kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel