Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari

Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari

- Kotun daukaka kara da ke Sokoto ta samu, Ciyaman din SUBEB, Murtala Adamu Jengebe da laifin karkatar da kudade

- Kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 41 sakamakon samunsa da aikata laifuka 7

- A baya, wata karamar kotu ta wanke shi daga zargin hakan yasa hukumar EFCC ta daukaka karar zuwa babban kotun da ke Sokoto

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Sokoto karkashin jagorancin mai shari'a Hannatu Sankey ta yankewa ciyaman din Hukumar Kula da Karatun Frimari na jihar (SUBEB), Murtala Adamu Jengebe hukuncin zaman gidan yari na shekaru 41.

Kotun ta yankewa Mr Jengebe hukuncin ne bayan ta same shi da laifuka bakwai cikin laifuka 10 da ake tuhumarsa da farko amma babban kotun tarayya na Gusau a jihar Zamfara ta wanke shi daga zargin.

Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari
Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Badakalar N29bn: Yadda wasu shaidu a tuhumar Nyako su ka yi mutuwar ban mamaki

Kotun daukaka karar tayi watsi da hukuncin da mai shari'a Habeeb Abiru na Kotun Tarayya na Gusau ya yi.

Kotun daukaka karar ta ce hukumar EFCC ta gabatar da hujjoji da suka gamsar da ita cewa ya aikata laifuka 7 cikin 10 da ake tuhumarsa da shi masu alaka da karkatar da kudade. An yanke masa hukuncin shekaru 5 a kowanne laifi guda sai dai za a lissafa shekarun zaman gidan yarin nasa a lokaci guda.

A ranar 12 ga watan Mayu, kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Gusau karkashin jagorancin mai shari'a Z.b. Abubakar ta wanke wanda ake tuhumar daga zargin aikata laifuka 10 masu alaka da karkatar da kudi.

Saboda rashin gamsuwa da hukuncin da karamar kotun tayi, hakan yasa hukumar EFCC ta daukaka karar zuwa kotun daukaka kara inda ta bukaci ayi watsi da hukuncin karamar kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel