An kama 'yan fashi da 'yan kungiyar tsafi 23 a jihar Kogi

An kama 'yan fashi da 'yan kungiyar tsafi 23 a jihar Kogi

A yau, Laraba ne 'yan sanda a jihar Kogi su kayi bajekollin wasu mutane 23 da ke zargi da aikata miyagun laifuka da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane da kafa kungiyoyin asiri.

An kuma ce an kama su dauke da bindigogi na kasashen waje guda 9 da wasu muggan mukamai.

A yayin gabatar da wadanda ake zargin a Lokoja, kakakin hukumar yan sandan jihar, William Aya ya ce akwai masu garkuwa da mutane 5, 'yan kungiyar asiri 5 da masu fashi da makami 13.

Ya ce biyu daga cikin wadanda ake zargi da fashi da makami, Jacob Ufedoh da Abubakar Zadiq daliban kwallejin kimiyya na jihar Kogi ne yayin da wani Paul Atobo kuma an kama shi ne wa wata guda bayan ya fito daga gidan yari.

An kama 'yan fashi da kungiyar tsafi 23 a jihar Kogi

An kama 'yan fashi da kungiyar tsafi 23 a jihar Kogi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Badakalar N29bn: Yadda wasu shaidu a tuhumar Nyako su ka yi mutuwar ban mamaki

A cewar Mr Aya, Mr Atobo, Ukwumdu Agono, Ebeh Musa, Ameh James, Ahmed Adams, Musa Mansur, AbdulHakeem Oyiza da Faruk Apasi an kama su ne yayin da suke fashi a Ayingba, Idah da Lokoja.

Kakakin yan sandan ya ce, su kuma Abubakar Ali, Yusuff Adamu, Seidu Adamu, Abdulkadir Adamu da Mati Sule an kama su ne saboda sace wani Mohammmed Bello a Fulani Camp a kauyen Osara a ranar 15 ga watan Nuwamba.

Mr Aya ya ce wadanda ake zargi da laifin sun kira iyalan wanda suka sace inda suka bukaci a biya su miliyoyin naira a matsayin kudin fansa amma 'yan sanda suka damke su kafin a kaiga biyan kudin.

An kuma kama mambobin kungiyar asiri na 'Aro Baga' bisa zarginsu da kai hari a ofishin yan sanda da ke Adankolo a Lokoja a ranar 17 ga watan Nuwamba.

Wadanda ake zargin sune Babangida Ibrahim, Shitu Jubril, Mola Samuel, Stephen Samson and Emmanuel Simon duk mazauna unguwar Adankolo a Lokoja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel