Boko Haram: Buhari zai gana da shugabannin kasashe 5 a Kasar Chadi

Boko Haram: Buhari zai gana da shugabannin kasashe 5 a Kasar Chadi

Za ku ji cewa a gobe Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai gana da wasu shugabannin kasashe biyar na nahiyyar Afirka a babban birnin N'Djamena na kasar Chadi dangane da ruruma da sake kunno kai na kungiyar ta'adda ta Boko Haram.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, kakakin fadar shugaban kasa Mista Femi Adesina, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a fadar Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Mista Adesina ya bayyana cewa, shugaba Buhari bayan kiran wannan zaman ganawa da juna cikin gaggawa, zai kuma jagoranci taron bisa ga martaba ta kasancewar sa shugaban Majalisar shugabannin kasa kuma jagora na cibiyar gwamnatin tafkin Chadi ta LCBC (Lake Chad Basin Commission).

Boko Haram: Buhari zai gana da shugabannin kasashe 5 a Kasar Chadi

Boko Haram: Buhari zai gana da shugabannin kasashe 5 a Kasar Chadi
Source: Depositphotos

Kakakin ya ci gaba da cewa, taron ganawar da zai gudana cikin wuni guda zai yi sharar fagge gami da tattaunawa kan al'amurran tsaro a yankunan da ta'addancin Boko Haram ke ci gaba da tayar da zaune tsaye.

Ganawar shugabannin kasashen za ta dabbaka tsare-tsaren kawo karshen wannan annoba ta ta'addaci Boko Haram musamman a bangaren inganta harkokin gudanarwa na kungiyar dakarun sa kai domin ci gaba da tunkarar barazana ta ta'addanci.

KARANTA KUMA: Gobarar Dare ta lankwame Daki 1, Shaguna 7 a jihar Kano

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, shugabannin kasashen da ke karkashin Majalisar LCBC da suka hadar da na Chadi, Kamaru, Nijar da kuma kasar Afirka ta Tsakiya za su halarci wannan taro.

Kazalika shugaban kasar Jamhuriyyar Benin da kawowa yanzu kasar sa ba ta gaza ba wajen bayar da gudunmuwar dakarun soji ya samu goron gayyata na halartar taron da shugaban kasa Buhari zai jagoranta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel