Ina gwanin wani ga nawa: Bahaushe, Musulmi, bakar fata ya lashe zaben kansila a kasar Amurka

Ina gwanin wani ga nawa: Bahaushe, Musulmi, bakar fata ya lashe zaben kansila a kasar Amurka

Haka Allah ke lamarinsa ba tare da neman izinin kowa ba, a yayin da shugaban kasar Amurka ke yaki da kwararan baki zuwa kasar Amurka, musamman ma bakaken fata, sai gashi an samu wani mutumi, Pious Ali ya zama kansila a wata karamar hukumar jaha dake kasar Amurka.

Gidan rediyon BBC Hausa ta ruwaito Pious Ali musulmi ne bakar fata, kuma bahaushe, amma dan asalin kasar Ghana, kuma ya zama kansila ne a majalisar karamar hukumar birnin Portland na jahar Maine.

KU KARANTA: Tsananin matsin rayuwa ta kai wani ma’aikacin gwamnati ga rataye kansa da kansa har lahira

Ina gwanin wani ga nawa: Bahaushe, Musulmi, bakar fata ya lashe zaben kansila a kasar Amurka
Pious Ali
Asali: Facebook

Tun a shekarar 2016 ne aka zabi Malam Pious a wannan mukami nasa, sai dai yace ire iren ayyukan da yayi a baya ne a sha’anin cigaban ilimi a garin a lokacin dayake aiki da hukumar ilimi ne yasa ya samu nasara, kamar yadda majiyar Legit.com ta ruwaito.

A cewar Malam Pious Ali; “An zabeni ne saboda jama’a sun lura da ayyukan da nayi a baya, don haka sun fahimci aikace aikacen da nake yi ina yinsu ne don taimaka ma kananan yara, na san wannan ya taimakeni kwarai da gaske.”

A lokacin da Pious ya lashe wannan zabe, hakan ya baiwa jama’a da dama mamaki, duba da manufofin shugaban kasar Amurka, Donald Trump, na hana bakaken fata shiga Amurka ko kuma korarsu ma gaba daya.

A hannu guda kuma, bayan kimanin shekara daya da samun nasarar Pious, sai wata mata yar asalin kasar Somalia ta yi ta maza, inda ta lashe zaben dan majalisa a kasar Amurka a shekarar 2017, inda ta zama yar majalisa mai wakiltar jahar Minnesota a majalisan wakilan jahar Amurka.

Sunan wannan Mata Ilhan Omar, kuma an haifeta ne a shekarar 1982 a garin Raas Cabaad na kasar Somalia, itace mace ta farko yar asalin kasar Somali da aka taba zama kowanni irin mukami a tarihin kasar Amurka gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel