Gobarar Dare ta lankwame Daki 1, Shaguna 7 a jihar Kano

Gobarar Dare ta lankwame Daki 1, Shaguna 7 a jihar Kano

Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta bayyana cewa, aukuwar wata wutar gobara ta lankwame Daki 1 da kuma Shaguna 7 a babbar hanyar Weatherhead da ke unguwar Sabon Gari a tantagwaryar birnin Kanon Dabo.

Alhaji Sa'idu Muhammad, kakaki hukumar ta kwana-kwana, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da 'yan jarida na kamfanin dillacin labarai a yau Laraba cikin birnin Kano.

Kakakin ya bayyana cewa, tsautsayin ya auku ne da misalin karfe 2.19 na daren yau Laraba da kawowa yanzu ba bu tabbaci dangane da adadin dukiya da ta salwanta.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito sun bayyana cewa, wannan tsautsayi na wutar Gobara ya lashe Daki daya da kuma Shaguna bakwai a unguwar Sabon Gari da ke karkashin karamar hukumar Fagge ta jihar.

Gobarar Dare ta lankwame Daki 1, Shaguna 7 a jihar Kano
Gobarar Dare ta lankwame Daki 1, Shaguna 7 a jihar Kano
Asali: Facebook

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gaggawar tunkarar wannan lamari daga bangaren hukumar kwana-kwana ta taimaka kwarai da aniyya wajen takaita ta'adi na wannan gobara wanda da tuni labari ya sha bamban.

KARANTA KUMA: Harin Maitile: Mun killace dukkanin Gawarwakin Dakaru - Hukumar Sojin Kasa

Cikin wani rahoton makamacin wannan, wutar Gobara ta yi mugun ta'adi cikin wani Gida da ke daura da kan Titin Bello a jihar ta Kano.

A sanadiyar haka hukumar Kwana-kwana na gargadin al'umma kan sanya idanun lura da kuma kiyaye harkokin su na gudanarwar yau da kullum yayin gabatowar yanayi da hunturu da annobar Gobara ke yawaitar aukuwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel