Harin Maitile: Mun killace dukkanin Gawarwakin Dakaru - Hukumar Sojin Kasa

Harin Maitile: Mun killace dukkanin Gawarwakin Dakaru - Hukumar Sojin Kasa

Mun samu cewa hukumar dakarun sojin kasa ta bayar da sanarwa kwashe dukkanin gawarwakin dakarun soji da rayukansu suka salwanta a yayin mummunan hari na kungiyar ta'adda ta Boko Haram da ya auku cikin sansanan dakaru da ke garin Maitile a jihar Borno.

Hukumar dakarun sojin ta bayar da wannan sanarwa cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na zauren sada zumunta sakamakon rahotanni da ke yaduwa kan cewa hukumar sojin ta nuna halin ko in kula ga gawarwakin dakaru da suka riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Sahara Reporters a jiya Talata ta ruwaito cewa, kawowa yanzu ba a killace gawarwakin dakarun soji da kuma na dakarun kungiyar sa kai da suka riga mu gidan gaskiya bayan aukuwar harin kwanaki kadan da suka gabata.

Harin Maitile: Mun killace dukkanin Gawarwakin Dakaru - Hukumar Sojin Kasa
Harin Maitile: Mun killace dukkanin Gawarwakin Dakaru - Hukumar Sojin Kasa
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, aukuwar wannan mummunan hari ya salwantar da akalla rayukan dakarun soji 120 yayin da mayakan kungiyar ta'adda suka yiwa sansanansu kwantan bauna cikin kauyen Maitile da ke karamar hukumar Gobar a jihar Borno.

KARANTA KUMA: Rashin Wutar Lantarki: Gwamna Obaseki ya fatattaki daya daga cikin manyan bakinsa cikin bacin rai

A yayin jaddada karamcinta ga dakarun sojin da ajali ya katsa masu hanzari, hukumar sojin cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na sada zumuntar Facebook ta bayyana cewa, ta aika da ayarin dakaru garin Maitile bayan aukuwar harin domin yawan lalube na killace gawarwakin dakaru da suka riga mu gidan gaskiya.

Cikin wani rahoton na daban, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar sojin sama ta Najeriya ta samu nasarar tarwatsa wani sansanin mayakan Boko Haram a garin na Maitile inda akalla rayukan 'yan ta'adda 213 suka salwanta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel