Gwamna Ganduje ya yi furuci kan Bidiyonsa na zargin karbar rashawa

Gwamna Ganduje ya yi furuci kan Bidiyonsa na zargin karbar rashawa

Mun samu rahoton cewa gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi furuci gami da karin haske dangane da dalilai na yada faifan bidiyon da ke haskaka zarginsa kan karbar cin hanci da rashawa a hannun 'yan kwangila.

Ganduje ya bayyana cewa, ba bu wasu dalilai na yada wannan faifayen bidiyo face wata kitimurmura ta shirya ma sa gadar zare domin hana shi samun nasara a babban zabe na 2019.

Kamar yadda shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa wannan kitimurmura ba za ta yi tasirin da 'yan adawa suka kudirta ba domin kuwa ba bu makawa sai yayi nasara a zaben na badi.

Gwamna Ganduje ya yi furuci kan Bidiyonsa na zargin karbar rashawa
Gwamna Ganduje ya yi furuci kan Bidiyonsa na zargin karbar rashawa
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamna Ganduje ya yi wannan furuci yayin karbar bakuncin kungiyar wasu 'yan kasuwa da suka ziyarce shi har fadarsa da ke Unguwar Nasarawa a Kanon Dabo.

Ko shakka ba bu wannan shine karo na farko da Gwamna Ganduje ya yi furuci a bainar jama'a tun yayin bayyanar faifan bidiyon kan zargin rashawa da ke haskaka shi yayin da yake tsaka da totse aljihun shakwararsa da makudan kudi.

KARANTA KUMA: Gwamna Yari ya dakatar da Sarakunan Gargajiya 4 a jihar Zamfara

Ganduje ya bayyana cewa, yada wannan faifan bidiyo wata kitimurmura ce ta 'yan adawa da kuma 'yan hamayya da ba bu wata nasara da za su cimma domin kuwa Hausawa na cewa kaikayi kan koma kan mashekiya.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tuni dai gwamnatin ta Kano ta shigar da karar kamfanin jaridar da ya fara wallafa wannan zargi da tuhuma, inda ta yi korafin ana neman bata mata suna a idon duniya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel