Katankatana: Wani Mutum ya bude wuta a kotu, ya kashe matarsa da surukinsa
A ranar Litinin 26 ga watan Nuwamba ne wani mutumi ya bude wuta da bindiga a wata kotu dake garin Durban na kasar Afirka ta kudu, inda ya kashe matarsa da kaninta, watau surukinsa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Majiyar Legit.com ta ruwaito lamarin ya faru ne a hawa na takwas na kotun, inda ma’auratan suka shigar da kara don neman kotu ta raba auren nasu saboda zaman aure a tsakaninsu yaki dadi.
KU KARANTA: Jiragen dankaro guda 32 sun nufo Najeriya dauke da man fetir da kayan masarufi
Kaakakin rundunar Yansandan yankin, Kanal Thembeka Mbele ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace “da misalin kerfe 11 na safe ne mutumin ya bude wuta yayin da Alkalin kotun ya bada hutun shan iska na yan mintoci, nan take ya kashe matarsa da kaninta.
“Shima yayi kokarin kashe kansa da kansa ta hanyar bindige kansa, amma bai samu nasara ba, inda a yanzu haka yana asibiti cikin mawuyacin hali.” Inji Kaakaki Thelma.
Jim kadan bayan faruwar harin sai ga jami’in tsaro sun mamaye kotun, inda aka hangesu suna fitar da Alkalai, akawu da sauran ma’aikatan kotun, wadanda daga ganinsu kasan suna cikin damuwa da kaduwa.
Sai dai wannan lamari ya dauke ma mahukunta kai da sauran jama’an kasar, saboda kotuna a kasar Afirka ta kudu na samun tsaro sosai da sosai, wanda hakan yasa kowa sai ya bi ta kofa mai binciken karafa a jikin mutum don gudun irin haka.
Anan gida Najeriya kuwa, wata babban kotun jahar Filato dake zamanta a garin Jos ta yanke ma wani matashi dan shekara 24 mai suna Godwin Banchir hukuncin kisa ta hanyar rataya biyo bayan kamashi da laifin kashe mahaifiyarsa yar shekara 65 da yayi.
Aa ranar Litinin 26 ga watan Nuwamba ne Alkalin kotun, mai sharia Daniel Longji ya yanke ma matashi Banchir hukuncin kisa akan kisan mahaifiyarsa Saratu Banchir da yayi, wai kawai don bata amsa gaisuwar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng