An kori mutum 50 daga ofishin jakadancin Najeriya a Ingila, ko me yayi zafi?

An kori mutum 50 daga ofishin jakadancin Najeriya a Ingila, ko me yayi zafi?

- An kori ma'aikata sama da 50 a ofishin jakadancin kasar nan a kasar Ingila

- An nemi dasu karbi takaddar barin su aiki a ranar 23 ga watan Nuwamba

- An koresu ne saboda sun nemi a biyasu albashin su

An kori mutum 50 daga ofishin jakadancin Najeriya a Ingila, ko me yayi zafi?
An kori mutum 50 daga ofishin jakadancin Najeriya a Ingila, ko me yayi zafi?
Asali: Facebook

Wani rahoto ya bayyana cewa an kori ma'aikatan Najeriya sama da 50 a birnin London, masu aikin jakadanci maqale da Ministare ta huldar kasashen waje dake Abuja.

Rayuwa dai na da tsanani idan mutum ya rasa aikinsa, kuma akwai alamar asiri zai tonu tunda ba a kasar su suke ba.

Bayan sallamar tasu an nemi dasu karbi takaddar barin su aiki a ranar 23 ga watan Nuwamba.

Kafin yanzu dai ma'aikatan sun bayyana cewa ba'a biyasu albashin wannan shekara 2018 ba gaba daya, inda takaddar kokar ke nuni da cewa an sallame sune a dalilin rigima da sukeyi akan ayi maza a biya su albashin su.

DUBA WANNAN: Atiku ya wahal damu saboda cuwa-cuwarsa - Oby Ezeks

Daya daga cikin ma'aikatan da aka kora yace" suna bukatar duniya taga yanda akayi musu rashin adalci aka koresu dan kawai sun nemi a biyasu hakkinsu".

Sannan sunyi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da yayi duba akan lamarin su.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng