Gwamnan jahar Kebbi zai saya ma hakimai da dakatai motocin alfarma

Gwamnan jahar Kebbi zai saya ma hakimai da dakatai motocin alfarma

Gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu ya bada umarnin gwamnatin jahar ta siyo motocin da za’a raba ma Hakimai da dakatan dake mulkin kananan hukumomin jahar guda ashirin da daya, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban kungiyar shuwagabannin kananan hukumomin jahar, ALGON, Shehu Marshal ne ya bayyana a ranar Juma’a bayan wata ganawar sirri da yayi da gwamnan jahar da sauran shuwagabannin kananan hukumomin jahar a Birnin Kebbi.

KU KARANTA: Yadda kasurgumin dan fashin daya jagoranci harin Offa ya mutu a hannun Yansanda

Marshal wanda shine shugaban karamar hukumar Jega ya bayyana ma manema labaru cewa gwamnatin jahar ta dauki gabaran sayo ma hakimai da dakatai motocin ne domin taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, musaman game da harkar tsaro.

“Hakimai da dakatai nada matukar muhimmanci wajen lamarin tsaro saboda sun fi kowa kusanci da jama’ansu, musamman ma wadanda suke yankunan karkara, don haka mukaga dacewar a saya musu ababen hawa don saukaka musu zirga zirga.” Inji Shehu Marshal.

Bugu da kari, shugaban karamar hukumar Jega, Shehu Marshal yace gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu ya amince a kananan hukumomi su biya gajiyayyu da marasa galihu naira dubu goma goma ga duk mutum daya don taimaka ma halin da suke ciki.

Majiyarmu ta ruwaito duk shuwagabannin kananan hukumomin su ashirin da daya sun halarci wannan zama da suka yi da gwamna a fadar gwamnatin jahar dake garin Birnin Kebbi.

A wani labarin kuma, uwargidar gwamnan jahar Kebbi, Zainab Bagudu ya bayyana cewa kasha sittin cikin dari na kananan yara dake jahar Kebbi na cikin rashin samun isashshen abinci mai gina jiki, wanda hakan kuma barazana ce ga kiwon lafiya a jahar.

Hajiya Zainab, wanda ita kanta likita ce ta bayyana haka ne a yayin kaddamar da ranar kula da jarirai da masu jego ta duniya na shekarar 2018 da aka yi a karamar hukumar Jega, inda tace alkalumman sun bayyana an samu ci baya a harkar samar da abinci mai gina jiki ga yara a jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel