Dubun wani Malamin Islamiyya dake danne kananan dalibai a gidansu ta cika a Kano

Dubun wani Malamin Islamiyya dake danne kananan dalibai a gidansu ta cika a Kano

Dubun wani Malami da ake kira da suna Ya Sayyadi ta cika, inda ya fada komar jami’an rundunar Yansandan jahar Kano sakamakon kamashi da suka yi da laifin zakke ma wata karamar yarinya dalibarsa, tare da yin lalata da ita.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Ibrahim Rabiu Kurna ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda yace a ranar Laraba 22 ga watan Nuwamba ne rundunar Yansandan jahar Kano ta kama Ya Sayyadi da wannan laifi.

KU KARANTA: Abota ta zama kiyayya: Wani mahauci ya kashe abokinsa da duka daya a Jigawa

Majiyar Legit.com ta ruwaito da fari dai wani mutumi ne ya dauki Ya Sayyadi mazaunin unguwar Dakata da ya dinga yi ma yayansa guda bakwai darasin Al-Qur’ani a gida, wanda aka fi sani da suna Lesson, inda shi kuma ya ci amanar da aka bashi.

Da yake yi wa Yansanda jawabi, Ya Sayyadi yace a lokacin da suke cikin bitan karatun ne sai dalibar tasa mai shekaru takwas ta fada masa cewa tana son ta yi rubutu, saboda haka sai ya daga yarinyar don ya daga yarinyar zuwa kan kujera, daga nan ne ya zakke mata.

Sai dai Ya Sayyadi ya bayyana damuwarsa da faruwar wannan lamari, inda yace kaddarace kawai Allah ya saukar masa, kuma a cewarsa bai taba aikata laifin ba, balle kuma ma ace da karamar yarinya, sa’annan ya nemi afuwan iyayen yarinyar.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, SP Magaji Musa Majia ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yayi kira ga iyaye dasu dinga lura da mutanen da zasu baiwa amanar yayansu, musamman malamai masu koyar dasu karatun addini dana boko.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng