Abota ta zama kiyayya: Wani mahauci ya kashe abokinsa da duka daya a Jigawa
Rundunar Yansandan jahar Jigawa ta yi carafken cafke wani matashi mai sana’ar Fawa, watau Mahauci, Aminu Umar mai shekara Talatin, 30 a rayuwa da laifin kisan kai bayan ya kashe abokinsa, Sani Bala mai shekaru 25 a abbatuwa, inji rahoton Daily trust.
Majiyar Legit.com ta ruwaito rikici ya fara kaurewa ne tsakanin mahautan biyu akan wanene a tsakaninsu ya kamata ya fede wani bunsuru da aka yanka, inda Aminu ya ja, Sani Bala ma ya ja, daga nan suka kaure da fada.
KU KARANTA: Babban abinda ya kai mu fadar shugaban kasa wajen Buhari – Gwamnonin jihohin Inyamurai
Sai shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar ba a wani dauki tsawon lokaci ana kiki kaka ba, saboda farawa da iyawa Aminu ya dunkule hannu ya kai ma Sani Bala naushi, shi kuma nan take ya fadi matacce ba ko shurawa.
Amma wata majiya ta daban ta yi karin haske akan dalilin fadan, inda tace cacar baki ce aka fara a tsakanin mahautan biyu akan yadda zasu raba canjin naira dari da aka biyasu bayan wani aiki da suka yi, a sanadiyyar haka ne Aminu ya dunkula ma Sani naushi har sai daya mutu.
Shaidun gani da ido da wadanda abin ya faru a gabansu sun bayyana cewar ganin halin da Sani Bala ya shiga ne suka bazama wajen mikashi zuwa Asibiti, inda a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Sai dai kaakakin rundunar Yansandan jahar Jigawa, SP Abdul Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma yace jami’an Yansanda sun samu nasarar kama Aminu a lokacin da yayi kokarin tserewa, sa'annan yace zasu gurfanar da shi gaban Kotu bayan kammala bincike.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng