Arangama tsakanin Makiyaya da Manoma ta salwantar da Rayuka 10 a jihar Katsina

Arangama tsakanin Makiyaya da Manoma ta salwantar da Rayuka 10 a jihar Katsina

Mun samu cewa kimanin rayukan Mutane 10 ne suka salwanta yayin da aka gwabza a wani sabon rikici tsakanin Makiyaya da Manoma a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, Sarkin Katsina Dakta Abdulmumin Kabir Usman, shine ya bayyana wannan mummunan rahoto na ban takaici a ranar Larabar da ta gabata.

Sarkin ya yi wannan furuci a fadarsa yayin da ya karbi bakuncin wata kungiyar da ke shawagin wayar da kawunan al'umma kan illolin ta'ammali da muggan kwayoyi, fyade, da kuma cin zarafi da keta haddin mata ta Queen Dijah Women and Children Awareness Initiative.

Uban na kasa ya bayyana cewa, illar ta'ammali da muggan kwayoyi ce ta yi tasiri kan miyagun mutanen da suka zartar da wannan mummunan ta'addanaci a jihar da ko shakka ba bu ta kasance Mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Arangama tsakanin Makiyaya da Manoma ta salwantar da Rayuka 10 a jihar Katsina

Arangama tsakanin Makiyaya da Manoma ta salwantar da Rayuka 10 a jihar Katsina
Source: Depositphotos

A cewarsa, wannan mummunan lamari ya auku ne yayin da makiyaya na Fulani suka fantsama cikin wasu gonaki a karamar hukumar Safana inda suka sheke rayukan Mutane 10 a ranar Litinin din da ta gabata.

KARANTA KUMA: Ka shirya faduwa zabe kamar yadda ta kasance ga Jonathan - Timi Frank ga Buhari

A sanadiyar hakan Sarki Abdulmumin ya bayyana takaicinsa tare da sake gargari gami da jan kunne dangane da illolin ta'ammali da muggan kwayoyi da ba bu wata makoma da suke haifarwa face ta halaka.

A nata jawaban shugaba ta wannan kungiya, Hajiya Khadija Saulawa, ta bayyana cewa kungiyar ba za ta gaza ba wajen ci gaba da bayar da gudunmuwa ta shawarwari da kuma wayar da kai kan barazana da kuma kalubalai da ke da nasaba da ta'ammali da muggan kwayoyi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel