Dandalin Kannywood: Daraktan daya shirya gadar zare, gagare, sangaya ya rasu
Mutuwa rigace bata fita, kamar yadda wani mawakin Hausa yake fada a cikin wakarsa, wannan tabbas ne, kuma hakan ya tabbata akan shahararren ma shiryin shirya fina finan Hausa da aka fi sani da Kannywood, Aminu Muhammad Sabo.
Legit.com ta ruwaito marigayi Aminu shine shugaban fitaccen kamfanin shirya fina finan Hausa, Sarauniya Film Production, ya rasu ne a ranar Talata 20 ga watan Nuwamba a jahar Kano bayan wata doguwar jinya da yayi.
KU KARANTA: Da dumi dumi: Gwamna Tambuwal ya bayyana sunan sabon mataimakinsa a Sakkwato
Ga duk masu bibiyan fina finan Hausa zasu yarda idan aka ce babu kamar kamfanin Sarauniya Films wajen shirya kayatattun fina finai masu nishadantarwa, ilimantarwa da kayatarwa a wancan zamani da masana’antar ke tatata.
Wasu daga cikin fina finan da marigayi Aminu ya shirya ko ya bada umarni sun hada da Gadar zare, Sangaya, Gagare, Tantiri, Diskindaridi, Nagari, Allura da zare, Garwashi da makamantansu, wanda dukkaninsu fina finan Sarauniya ne.
Da wannan za’a iya tabbatar da cewar mamacin ya bada muhimmiyar gudunmuwa a fagen Kannywood ta wajen bunkasa masana’antar tare da habbakata zuwa matsayin data kai a yau.
Tuni aka gudanar da jana’izar Aminu a ranar Larab 21 ga watan Nuwamba, jana’izar da daruruwan masoya da taurarin Kannywood suka samu halarta, kuma a can aka binneshi a jahar Kano. Allah Ya jikansa da gafara.
An samu mace mace da rashe rashen wasu daga cikin manyan taurarin masana’antar Kannywood, wasu daga cikin mamatan sun hada da Rabilu Musa Ibro, Kulu, Yautai, Kasimu Yero, Aisha Dankano, Umar Waragis da dai sauransu, da fatan Allah ya jikansu duka.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng