Anyi zanga-zanga a makarantar da aka rufe saboda dalibai sun saka hijabi

Anyi zanga-zanga a makarantar da aka rufe saboda dalibai sun saka hijabi

- Iyayen yaran makarantar sakandire ta jami'ar Ibadan da aka rufe kwanakin baya sunyi zanga-zanga a ranar Laraba 21 ga watan Nuwamba

- Iyayen sun bukaci mahunkanta makarantar su suyi watsi da bukatar da wasu ke nema na cewa sai dalibai musulmai sun rika sanya hijabi

- A cewarsu, wannan yunkuri ne na jefa kyama da kiyaya tsakanin daliban da suka taso suna karatu da wasa tare na tsawon shekaru

Wasu daga cikin iyayen daliban makarantar Sakandire na Jami'ar Ibadan sunyi zanga-zangar nuna rashin amincewa da bukatar da wasu iyayen dalibai musulmai suka gabatarwa makarantar na neman a bari 'ya'yansu su rika sanya hijabi inda suka ce hakan zai raba kawunnan daliban makarantar.

Iyayen sun ziyarci makarantar a yau Laraba dauke da kwalaye masu rubutu inda suka nufi ofishin mataimakin shugaban jami'an, Farfesa Abideen Aderinto kuma suka mika masa wasikarsu da ke dauke da sakon rashin amincewarsu da saka hijabin wadda hakan ya janyo aka rufe makarantar a ranar Litini da ta gabata.

Iyayen yara sunyi zanga-zangar rashin amincewa da saka hijabi
Iyayen yara sunyi zanga-zangar rashin amincewa da saka hijabi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda Jega ya yi amfani da INEC wajen kayar da ni zabe - Jonathan ya yi fallasa a sabuwar littafinsa

Jagoran zanga-zangar, Barrister Olalekan Thani, Babaawo Awosanmi Abe da Olusola Alesin sun ce bai kamata a bari wasu kungiyoyin mutane su raba kan dalibai a makarantar da aka kafa ta tun shekaru 55 da suka shude ba.

Sun ce matakin fara sanya hijabin zai sanya kananan yaran su taso suna kyamar junansu saboda banbanci addini ko wani abu mai kama da haka a maimakon su tashi a matsayin 'yan kasa daya.

A wasikar da suka rubuta mai taken 'Clamour for the Introduction of Religious Emblem of Our Children in the International School, University of Ibadan,' iyayen sun bukaci mahukuntar makarantar su tabbatar dukkan iyayen sun cigaba da biyaya da dokar makarantar da kowa ya amince da ita yayin da ya saka 'ya'yansa.

Sun zargi iyayen yaran da ke kokarin yaransu sai sun fara saka hijabi da yunkurin kawo cikas ga karatun daliban da kuma kauna da zaman lafiya da ke tsakanin daliban da ba su ganin banbanci tsakaninsu saboda addini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164