Ba zan manta da yan Fim, mawaka da yan nanaye ba – Inji Atiku Abubakar

Ba zan manta da yan Fim, mawaka da yan nanaye ba – Inji Atiku Abubakar

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019 zai tabbatar da cewar bai bari bangaren nishadi na Najeriya ba.

Legit.com ta ruwaito Atiku ya bayyana haka ne cikin wata takarda dake dauke da tsare tsaren da yake da burin aiwatarwa idan har ya zama shugaban kasar Najeriya, inda yace zai kare yan wasan kwaiwayo watau yan Fim, mawaka da sauran yan nanaye daga satar fasaharsu.

KU KARANTA: Yadda muka kakaba ma shugaban kasa Obasanjo takunkumi – Inji tsohon Gwamna Osoba

Takardar na kunshe da duk wasu aikace aikacen da Atiku ya kuduri aniyar gudanarwa a Najeriya a tsawon shekaru shida daga 2019 zuwa 20125, inda yayi nuni zuwa ga matsalar da ake samu a bangaren nishadantarwa, kuma yace zai magancesu.

Wasu daga cikin matsalolin da Atiku ya ambato sun hada da matsalar samun isassun kudaden gudanar da aikace aikacensu, satar fasaharsu, sayar da ayyukansu ba tare da izininsu ba, rashin sanin hanyoyin watsa kayansu a kasuwannin duniya, da kuma rashin samun sassaucin kudin haraji.

“Nayi alkawarin samar da tsare tsare, da kwararan dokokin da zasu samar da manyan kayayyakin aiki, isassun kudade, ingantaccen yanayin kasuwanci da gudunmuwa na musamman ta yadda bangaren nishadi zai bunkasa tare da samar da aikin yi ga matasanmu.” Inji shi.

A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya tabbatar da burinsa na sayar da kamfanin man fetir na Najeriya da matatun man fetir guda hudu na Najeriya gaba daya don samun isassun kudade a Najeriya.

Kaakakin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Segun Sowunmi bayyana haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace idan har Atiku Abubakar ya samu nasara a zaben 2019, zai sayar da matatun man fetir gaba daya, yan Najeriya zai sayar ma wa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng