Zan biya N50,000 mafi karancin albashi - Dan takarar shugaban kasa

Zan biya N50,000 mafi karancin albashi - Dan takarar shugaban kasa

- Mr Gbenga Olawepo-Hashim na jam'iyyar Peoples Trust ya yi alkawarin biyan N50,000 a matsayin alabashi mafi karanci idan ya lashe zabe

- Olawepo-Hashim ya ce gwamnonin Najeriya ba su son su rika biyan N30,000 ne saboda ba su da basirar kirkirar hanyoyin samar da kudi

- Dan takarar shugaban kasan ya kuma ce zai rika samar da ayyuka 4 miliyan a duk shekara a Najeriya idan aka zabe shi

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Trust (PT) Mr Gbenga Olawepo-Hashim ya bayyana cewa zai biya N50,000 a matsayin albashi mafi karanci a cikin shekararsa na farko kuma ai daukewa yan Najeriya dawainiyar duba lafiyarsu a kyauta.

Olawepo-Hashim ya fadi wannan abubuwan ne yayin kaddamar da yakin neman zabensa gabanin babban zaben 2019 a Abuja.

Zan biya N50,000 mafi karancin albashi - Dan takarar shugaban kasa
Zan biya N50,000 mafi karancin albashi - Dan takarar shugaban kasa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

A cewar dan takarar shugabancin kasar, gwamonin Najeriya ba su son su biya N30,000 a matsayin albashi mafi karanci saboda ba su da basira na kirkirar hanyoyin samar da kudaden shiga a jihohinsu.

Ya ce: "Ba su da basirar kirkirar hanyoyin samar da kudade, idan aka zabe mu, za mu biya N50,000. Haka ne kawai za a bawa 'yan Najeriya albashin da zai ishe su rayuwa.

"Najeriya na daya daga cikin kasashen da ake da riba ga masu saka jari, matsalar kawai shine akwai wasu mutane da ka hana ruwa gudu a tsakanin masu saka jarin da ma'aikata.

"Mun kashe dallan Amurka 7.8 tiriliyan wajen samar da kayayakin more rayuwa a duniya domin neman yadda za mu samu kudi."

Ya bayyana damuwarsa kan yadda Najeriya ke kashe kudade amma ba a samun wani riba da ke fitowa sakamakon saka jarin.

Ya cigaba da cewa zai samar da ayyuka miliyan 4 a duk shekara ta hanyar samar da yanayi mai kyau da zai janyo hankulan masu saka hannun jari na gida da kasahen waje su saka jari a kamfanoni da za su samar da ayyuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel