Harin ta’addanci: An kashe mutane 50 a yayin bikin maulidi
Akalla mutane hamsin ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar harin ta’addanci a aka kai ma wasu al’umma musulmai yayin da suke gudanar da bikin maulidin tunawa da ranar haihuwar annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.
Maharan sun kai wannan mummunan hari ne a garin Kabul na kasar Afghanistan a ranar Talata 20 ga watan Nuwamba wanda yayi daidai da ranar 12 ga watan Rabiul Awwal, ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad, kamar yadda tarihin Musulunci ya nuna.
KU KARANTA: Fasa taro: Shugaban APC Oshiomole ya rikirkita mahalarta bikn kaddamar da littafin Jonathan
Kaakakin ma’aikatan kiwon lafiya ta kasa, Wajid Majroh ya bayyana cewa baya da adadin mutanen da suka mutu, akwai wasu mutane saba’in da biyu da suka jikkata inda suka samu munanan rauni.
Legit.com ta ruwaito maharan sun kai harin kunar bakin wake ne da nufin kashe manyan malamai da shuwagabannin al’umma da suka halarci taron wanda ya gudana a wani dakin taro dake tsakiyan garin Kabul.
Wani malami daya halarci maulidin, Muhammad Hanif ya bayyana cewa suna cikin karatun Al-Qur’ani ne kwatsam sai suka ji wani kara daya cika musu kunnuwa, daga nan sai hargitsi ya biyo baya sakamakon kowa na kokarin tserewa daga harin.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sassan jikin mutane, jini, karyayyun kujeru da gilasan winduna sun mamaye dakin taron. Shugaban kasar Afghanista, Ashraf Ghani ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shiga damuwa matuka game da harin, don haka ya sanar da jimami a duk fadin kasar gaba daya.
Shugaba Ashraf ya tabbatar ma al’ummar kasar cewa ba gwamnatinsa ba zata yafe wannan harin ta’addanci ba, kuma za tayi duk mai yiwuwa wajen ganin ta kamo duk masu hannu cikin harin.
Sai dai har yanzu babu wata kungiyar ta’addanci da ta dauki nauyin kai wannan hari, ba kamar yadda aka saba a baya ba, inda kungiyar ta’addanci ta ISIS ko ta Al-kaida ke bayyana daukan nauyin kai duk wasu hare haren da suka kai.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng