Mummunan hatsari: Motar daukan yashi ta tattake dalibai Mata 3 a garin Funtua

Mummunan hatsari: Motar daukan yashi ta tattake dalibai Mata 3 a garin Funtua

Wani dan achaba mai tsananin ganganci yayi sanadin mutuwar wasu dalibai mata yan makarantar gwamnati ta mata dake garin Funtuwa ta jahar Katsina, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wannan mummunan hadari ya faru ne a daidai lokacin da dan achaban yayi kokarin shigewa gaban motar daukan yashin da akafi sani da suna Tantebir yayin da take tafiya akan titin Zaria dake garin Funtua.

KU KARANTA: Tashin hankali: Yadda wani ‘Da’u fataken dare’ ya yi awon gaba da Mota daga ofishin Yansanda

Sai dai wannan kokari na dan achaban bai cimmasa ba, inda yayin da yake kokarin shan gaban motar sai babur din ya kufce masa, inda nan take ya suka fada gaban motar, inda ta tattakesu gaba daya, daga daliban har dan achabar.

Majiyoyi sun tabbatar da sunayen daliban kamar haka; Maryam, Saadatu da Aisha Muhammad, inda suka yo goyon uku, kuma hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gidajensu dake unguwar Tudun Malamai a garin Funtua.

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace: “Dan achaban ne yayi kokarin shan gaban Motar tipan, amma bai samu sa’a ba, inda babur ta kufce masa, anan suka fadi gaban motar, wanda ta tattakesu duka.”

Tuni aka gudanar da jana’izar matan, sai dai babu tabbacin yadda aka yi da gawar dan achaban. Shima kaakakin hukumar kare haddura ta kasa reshen garin Funtua, Abdullahi Yau yace har zuwa lokacin tattara rahoton basu samu labarin hadarin ba.

Sai dai kaakakin ma’aikatan ilimi ta jahar Katsina, Lawal Kerau ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yayi addu’ar Allah ya jikan daliban da ma dan achaban, kuma Allah ya baiwa iyalansu hakurin rashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng