Karin albashi: Kungiyar kwadago ta ja kunnen shugaba Buhari
A jiya, Asabar, ne shugabannin kungiyar kwadago (NLC) su ka shawarci shugaba Buhari a kan bin ra'ayin gwamnonin Najeriya a kan batun karin albashin ma'aikata.
Da yake jawabi yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar Ekiti, Ayuba Wabba, shugaban kungiyar kwadago ya ce babu gudu, babu ja da baya a kan karin ma fi karancin albashi zuwa N30,000.
Wabba ya bayyana kurarin gwamnonin na cewa sai dai su rage yawan ma'aikata kafin su iya biyan karin albashin da cewar yunkurin janye hankalin NLC ne a kan batun karin albashin.
An shiga takun saka tsakanin kungiyar NLC da gwamnonin Najeriya ne a kan kafewar kungiyar ta kwadago a kan sai a inganta rayuwar ma'aikata ta hanyar yi ma su karin albashi.
A ranar Laraba, ne bayan kammala wata ganawa, gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar gwamnoni, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewar biyan N30,000 a matsayin ma fi karancin albashi ba abu ne mai yiwuwa ba.
Sannan ya kara da cewar gwamnoni za su iya biyan sabon albashin ne idan kungiyar kwadago za ta amince su rage yawan ma'aikatan jihohin su.
DUBA WANNAN: Kamfen: PDP ta shiga damuwa a kan tunkarar yankin kudu maso yamma
Sai dai kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi watsi da kurarin da gwamnonin Najeriya su ka yi kan cewar sai dai su rage yawan ma'aikata kafin su iya biyan N30,000 a matsayin ma fi karancin albashi.
Kungiyar ta ce barazanar gwamnonin ba sabuwa ba ce tare da bayyana cewar ma'aikatan Najeriya na nan a kan bakansu dangane da biyan N30,000 a matsayin ma fi karancin albashi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng