Faduwar tankar dakon man fetur ya haddasa mummunar gobara a Sokoto
Da tsakar daren jiya, Juma'a, ne misalin karfe 12:00 wata tanka makare da man fetur ta fadi kusa da sakatariyar karamar hukumar Gada, daidai gangaren mahadar Gada, kuma nan take ta kama da wuta.
Tashin gobarar ya yi sanadiyar konewar babban masallacin juma'a na kungiyar 'yan Izala (JIBWIS) na garin Ga da shagunan 'yan kasuwa da ma gidajen jama'a.
Sai dai jami'an hukumar kashe gobara bisa jagorancin kakakin majalisar dokoki ta jihar Sokoto sun yi nasarar kashe wutar tare da dakile yaduwar ta.
Kakakin majalisar dokokin ya jajantawa jama'ar garin Gada bisa wannan iftila'in da ya fada ma su tare da ziyartar asibiti domin duba wadanda su ka samu raunuka.
DUBA WANNAN: Musulman kabilar Igbo sun gabatar da bukatar su ga Buhari
Ana yawan samun tashin gobara sakamakon faduwar tankar dakon man fetur a Najeriya, musamman a jihar Legas.
Ko a kwanakin baya saida aka samu tashin wata mummunar gobarar a Legas, sanadiyar fadowar wata tankar dakon man fetur daga kan gadar Otedola a garin Legas.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng